'Yadda lalataccen abinci ya jawo mani shanyewar jiki'

Malcolm Brown

Asalin hoton, Malcolm Brown

Bayanan hoto, Malcolm Brown ya shafe watanni tara a asibiti
    • Marubuci, Daga Angie Brown
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Scotland News
  • An wallafa

Malcolm Brown ya dauka cewa yana fama da karancin ruwa ne kawai a jiki lokacin da kafafuwansa suka daina aiki bayan cin lalataccen abinci a kasar Turkiyya.

Amma a lokacin da hannaye da kafadunsa suka sage kana idanunsa suka dusashe, ya gane cewa akwai babbar matsala.

Daga nan ya gamu da shanyewar jikinsa daga wuya zuwa kasa.

An kai tsohon injiniyan asibiti a birnin Edinburgh, inda aka gano ya kamu da cutar da ke shafar jijiyoyin jikin dan Adam da ake kira Guillain-Barre syndrome.

Ya yi magana da BBC daga kan gadonsa na asibiti ta hanyar amfani da wata na'ura da ke daukar murya, saboda ba zai iya rike wayar salula ba.

Mai shekaru 71, ya bayyana yadda shi da matarsa Janis suka tafi Turkiyya don yin wani hutu a ranar 19 ga watan Satumbar bara.

Janis and Malcolm Brown

Asalin hoton, Janis Brown

Bayanan hoto, Janis da Malcolm Brown lokacin yawon hutun shakatawa a kasar Turkiyya kafin ya kamu da rashin lafiya

Amma kuma, Malcolm ya gamu da matsalar da ta shafi cin lalataccen abinci kuma ya shafe mako daya kwance yana fama da rashin lafiya.

Ma'auratan sun yi zaton wani cukwui da suka sayo a wani shago ne ya haddasa matsalar.

Malcolm ya kamu da rashin lafiya bayan da ya ci, amma Janis ba ta ci ko daya ba. Wani abokinsa shi ma da ya ci cukwui din ya kamu da rashin lafiya daga lalataccen abincin washegari.

A lokacin da suka dawo Edinburgh, Malcolm ya fara jin "jikinsa babu dadi" ya rika jin yatsunsa suna zugi kuma kafafunsa sun yi sanyi.

A cewarsa: "Na fito daga cikin mota na fadi a kan bayana a bakin hanya kuma na kasa tashi."

"Janis ce ta yi kokarin ta mirgino da ni na rika jan ciki. Daga nan ba na iya saka tufafi a jikina saboda ba zan iya motsawa ba don haka sai Janis ce take saka min tufafi.

"Ba na iya rike cokali in kai shi bakina ko butar dafa ruwa, a nan ne na fahimci cewa wani abu ne da ya wuce batun karancin ruwa.

"Jikina ya kara tabarbarewa cikin sauri kuma abin tsoro ne rashin sanin mene ne ya faru."

Malcolm Brown

Asalin hoton, Malcolm Brown

Bayanan hoto, Malcolm Brown kan yi wasan kwallon golf sau uku a ko wane mako kafin ya kamu da cutar

Malcolm ya ce wata rana lafiyarsa kalau, kana bayan nan ba ya iya yi wa kansa komai.

Ya kara da cewa: "Ban taba zaton wani abu zai yi min haka ba.

"Bangare mafi wahala shi ne amincewa da taimako daga ma'aikatan asibiti da kuma Janis. Ba na son dora wa Janis nauyi.

"Ta shafe shekaru 10 tana kula da iyayenta, don haka ba na son ta sake daukar wani nauyin. Ban damu da kaina ba, ya danganta da Janis wacce ita ce damuwa ta."

Janis ta ce "abin bakin ciki ne" ganin yadda jikin Malcolm ya shanye daga wuya zuwa kasa.

"Yakan fadi kasa kamar wani katon jariri kuma sai an sake dago shi a dora shi kan gado," in ji ta.

"Ba a amince wa 'yayanmu mata biyu su gan shi ba har na tsawon watanni tara.

"Abin tsoro ne. Ba a amince in ga Malcolm ba har na tsawon watanni biyar saboda dokar kullen korona."

Janis Brown

Asalin hoton, Janis Brown

Bayanan hoto, Janis Brown na gasar tseren mil 874 don samar da kudi ga kungiyar bayar da tallafi ta Gain

Janis ta kira Gain, kungiyar da ke tallafa wa masu fama da cutar ta Guillain-Barre syndrome don gano ko za ta iya sayen wata na'urar da za ta bai wa mijinta damar bugawa da kuma amsa waya ba tare da amfani da hannayensa ba.

"A lokacin ne suka nuna cewa za su dauki nauyin biyan na'urar daukar muryar.

"Na riga na biya, amma haka ya sa na fara tunanin yana da kyau a ce kungiyar agajin ta dauki nauyin irin wadannan abubuwa da zai taimaka wa mutane, don haka ina son samar musu da kudi."

Sakamakon haka Janis, mai shekaru 69, ta shiga gasar tsere tsakanin yankunan Lands End zuwa John O'Groats - na mil 874 - don hada wa kungiyar Gain kudi. Mil 10 kacal ya rage mata ta kammala.

Cutar na nufin cewa garkuwar jikin Malcolm na ta kai wa hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwarsa farmaki.

Ga mutane masu fama da cutar Guillain-Barre syndrome wani abu da bai kamata ba ne ke faruwa kuma a bisa kuskure yakan kai farmaki tare da lalata hanyoyin kwakwalwa.

Babu tabbaci kan ko me ya sa hakan ke faruwa, amma cutar takan faru ne idan kwayoyin cuta suka shiga hanyoyin numfashi, kamar su mura ko kuma kwayoyin cutar cikin mutum kamar wanda cin lalataccen abinci ke haddasawa.

Likitoci sun ce duk da cewa babu tabbaci kan girman lahani da cutar ta yi wa jijiyoyin kwakwalwar Malcolm, za su iya gyaruwa a tsakanin watanni 12 zuwa 18.

Malcolm Brown

Asalin hoton, Malcolm Brown

Bayanan hoto, Malcolm Brown ya ci kofin gasar wasan B Championship a filin wasan Golf a Swanston a shekarar 2019

Yanzu Malcolm ya kara murmurewa har yana iya tashi tsaye ya kuma zauna a cikin keken guragu.

"Har yanzu ba na iya motsa wuyan hannuna, don haka hannayena kan rika lilo a karshen kafaduna," a cewarsa.

"Ban zaci zai dauki tsawon lokaci kafin na samu waraka ba, amma ni mutum ne wanda ba ya yanke kauna kuma ban shiga tsananin damuwa ba ko zama abin tausayi."

"Har yanzu Malcolm a bukatar a rika na shi abinci a baki, kuma yana bukatar cikakkiyar kulawa ta kiwon lafiya, amma ya ce ya zama mai juriya game da rayuwarsa.

"Na amince cewa ba zan iya yin komai ba a yayin da nake asibiti, kuma ta hanyar nuna halayya mai kyau na san zan samu sauki," in ji shi.

"Na yi tunanin, in da a ce na dauki wani fakitin cukwui na daban daban samu kai na a nan ba ....amma dole ka aince da kaddara."

Iyalansa na cike da fatan zai dawo gida cikin wata ma zuwa da zarar an gina hanyoyin bi da keken guragu.

Kafin ya gamu da shanyewar jiki, Malcolm kan yi wasan kwallon sau uku a mako kuma ya kammala mil 25 na tseren keke.

Ya kara da cewa "ba lallai na zama mai kuzari irin yadda nake a baya ba, amma ba zan taba yanke kauna da komai ba."