Majalisar dattawa ta amince da kasafin kudin rundunar 'yan sanda a Najeriya

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da fiye da naira biliyan 74 a matsayin kasafin kudin shekarar 2021 na asusun amintattun na 'yan sandan kasar wato Police Trust Fund.
Hakan ya faru ne bayan amincewar da majalisun dokokin kasar suka yi wa wani rahoto kan harkokin 'yan sanda.
An kafa asusun ne don tabbatar da karin kayan aiki ga 'yan sandan Najeriya wadanda ke fama da karancin kudaden gudanarwa tsawon shekaru.
Shugaban kwamitin harkokin 'yan sanda na majalisar dattijan, Sanata Haliru Dauda Jika, shi ne ya gabatar da rahoton, ya kuma shaida wa BBC cewa kasafin kudin shi ne yake wakiltar kasa da kashi daya na harajin da ke zuwa babban asusun gwamnatin Najeriya.
''Wannan kudi ya kama Naira biliyan 74 da digo 7, manufar shi ne a samar wa 'yan sanda kayan aiki, da walwala da kara musu horo saboda yawanci idan suka yi horon farko ba a cika damuwa da ka ra ba su wani horo ba, domin haka wannan ma'aikata za ta kula da tabbatar da an yi hakan,'' in ji Dauda Jika.
Sanata Dauda kara da cewa yadda za a yi aiki da kudaden sun hada da hukumar 'yan sanda ta bai wa wannan asusu na Trust Fund, su bukaci su ba su bayanin abubuwan da su ke bukata, sai ita hukumar ta yi lissafi ka na ta mika hakan ga majalisa wadda ita kuma za ta aminta a fitar da kudin domin gudanar da ayyukan.
A cewarsa: ''A shekarar da ta gabata ba mu samu mun yi kasafin kudin baki day aba, don haka akwai Naira biliyan 22 da muka dauko muka kawo su gaba, amma in ba haka ba abin da za a samu ba zai wuce biliyan 50.
A shekarar 2020 da aka rantsar da hukumar da lokacin da suka fara aiki, ba a samu an yi akan lokaci ba da wasu abubuwa da suka shafi shari'a ta gwamnonin Najeriya da hukumar amintattu su na ganin jihohi na da asusu irin wannan shi ne dalilin da ya sa aka samu tsaiko.
Mataki na gaba da za mu dauka a majalisa hakkin mu ne mu tabbatar an yi amfani da abin nan da muka halatta, an kashe su yadda ya kamata, kan tafarkin da gwamnatin Najeriya ta aminta da shi."










