An gano ƙwarangwal ɗin mutanen da suka shekara dubu 100 da mutuwa a Isra’ila

    • Marubuci, Daga Pallab Ghosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent
  • An wallafa

Masu binciken da ke aiki a Isra'ila sun gano wani tsohon mutum da ba a san shi ba, wanda ya rayu tare da jinsinmu sama da shekaru dubu 100 da suka gabata.

Sun yi imanin cewa ragowar abubuwan da aka gano kusa da birnin Ramla na a matsayin sassan jikin mutanen da suka rayu a wancan lokacin.

Abubuwan da aka samo sun haɗar da ƙoƙon kai da muƙamuƙin mutumin da ya rayu tsakanin shekara dubu 140 da dubu 120 da suka wuce.

An buga cikakken bayanin a mujallar Kimiyya ta duniya.

Masu binciken suna kyautata zaton cewa mutumin ya fito ne daga jinsin farko wanda watakila ya bazu daga yankin tun daruruwan dubunnan shekaru da suka gabata kuma ya haifar da nau'in mutanen da aka yi zamaninsu a Turai da Asiya tun kusan shekaru dubu 40 da suka gabata da ake kira Neanderthals.

Su dai Neanderthals nau'in mutane ne da suka rayu can a baya, kamar su daya da ta mutane ba irin namu ba, domin akwai dan bambanci.

Masana kimiyyar sun sanya wa sabon nau'in da aka gano suna "Nesher Ramla Homo".

Tawagar na tunanin cewa nau'in mutanen sun rayu ne a Gabas ta Tsakiya shekaru 400,000 da suka wuce.

Masu binciken sun lura da kamanceceniyar da ke tsakanin mutumin da aka gano da kuma nau'in Neanderthal da suka rayu a turai.

"Akwai burbushin mutane da yawa daga kogon Qesem, da Zuttiyeh da Tabun wadanda suka dace da wancan lokacin wanda ba za mu iya danganta su ga wani sanannen rukunin mutane ba", a cewar masanan.

Daya daga cikinsu Dr May ta ce suna kyautata zaton cewa waɗannan mutane kakanni ne ga Neanderthals.

Masu binciken sun kafa hujja da kamanceceniyar da ke tsakanin burbushin nau'in tsoffin mutanen da aka gano a Isra'ila da wadanda aka samu a Turai da Asiya, duk da cewa furucin nasu yana da rikitarwa.

Farfesa Chris Stringer, daga Gidan Tarihin halitu na Landan, ya fara wani bincike a kwanan naya kan burbushin tsoffin mutanen China.

"Nesher Ramla na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa har yanzu jinsin halittu daban-daban sun kasance tare a yankin a lokaci guda kuma yanzu muna da labari irin wannan a yammacin Asiya," in ji shi.

"Duk da haka, ina ganin tsalle ne ya yi nisa a wannan lokacin don danganta wasu tsoffin burbushin bil adama a Isra'ila da Neanderthals," a cewarsa.

A cewar sakamakon wani bincike da Dr Yossi Zaidner ya yi a Jami'ar Urushalima, waɗannan kayan aikin an gina su ne kamar yadda mutanen baya suke yin kayan aikinsu.

Dr Zaidner ya ce "Abin mamaki ne cewa mutanen zamanin da suna amfani da kayan aikin da ke hade da Homo sapiens. Wannan yana nuna cewa akwai hulɗa tsakanin ƙungiyoyin biyu," in ji Dr Zaidner.