Bishiyar dabinon da ta wanzu zamanin Annabi Isa ta sake tsirowa a Isra'ila

An wallafa

Wannan hoto da kuke gani a sama, a nan ne ake da wata dadaddiyar bishiyar dabino mai tsohon tarihi. Kun san mene ne dalili? Saboda ta bace tun shekaru 2000 da suka gabata wato zamanin Annabi Isa, amma a yanzu kwatsam wasu mata biyu sun sake farfado da ita.

Yankin da bishiyar take, dama ya shahara wajen shukar dabino, amma lokacin da Romaniyawa suka je wajen shekaru 2000 da suka shude don mamaye shi, sai aka samu gagarumin rikici tsakaninsu da Yahudawan da ke rayuwa a wajen.

Sai da ta kai Yahudawan sun yanke shawarar cewa za su kashe kansu baki daya, amma kafin su yi haka sai suka banka wa dukkanin wuraren ajiye abinci da ke yankin wuta, amma ban da wani waje guda.

Babbar fargabarsu ita ce kada Romaniyawa su kama su su daure ko su mayar da su bayinsu.

Bayan shekaru 2000 wani masanin kimiyya a Isra'ila ya gano wasu yankunan wuraren ajiye abincin da aka kone tun a wancan lokaci,

A kusa da su ne kuma aka samu wasu nau'ukan tsirrai daban-daban.

An ajiye su a wani waje tsawon shekaru 40, har zuwa lokacin da wata mai bincike ta je domin a nuna mata wasu daga cikinsu.

A halin da ake ciki ana amfani da wasu daga cikinsu wajen neman lafiya, inda ake ake maganin damuwa, da kuma inganta sha'awa don saduwa, wannan abu ya zamo mai muhimmanci ga Isra'ila, sannan shi ma dabinon yana da muhimmanci a gare ta.

Kamar dai yadda Kasashen Yamma suka yi fintinkau wajen harkokin fasaha, haka ita ma Isra'ila ke alfahari da wannan dama da take da ita.

Samun wannan iri abu ne mai matukar wahala, ga bata lokaci ga kokarin nusantar da masu iko da su dalilin da ya sa kake son shi, idan suka tambaye ka ka ce musu kana so ka shuka ka rene su ne sai su ce maka lallai ba ka da hankali.

Dr Elaine Solaweire, darakta a fannin raya harkokin noma a Isra'ila da yar uwarsa Sara, sun bayyana cewa sun shuka irin wannan iri da suka samo, inda bayan wani lokaci kawai sai ta ga ya tsiro cikin sauri.

"Ban yi tunanin abin da hakan zai haifar ba, ko da na gaya wa wata yar uwa ta Sarah, sai ta ce me kika ce?, da na ce mata ya kike ganin za a yi yanzu?, sai ta ce ki kyale ta kawai."

Daga nan ne ta ci gaba da girma har zuwa wannan lokaci da aka sa mata sunan Methuselah.

A yanzu dai bayan shekaru 2000 da bacewar bishiyar ta farfado, har ma ana cin dabinon da take samarwa.