Ba a ga mutum 99 ba da ɓaraguzan gini mai hawa 12 ya danne a Amurka

Champlain Towers

Asalin hoton, Google Street View

Bayanan hoto, Ga yadda ginin yake kafin ya rushe
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Masu aikin ceto na ci gaba da binciken ko za a samu wanda za a ƙara ceto wa daga cikin ɓaraguzan gini mai tsayi 12 a arewacin Miami.

Akalla mutum daya ne aka tabbatar ya mutu a hukumance har yanzu kuma ana neman wasu 99.

Da yawan iyalai sun zaƙu su ji labarin 'yan uwansu, masu binciken da suke aiki ba dare ba rana sun ce suna jiyo ihun mutane a cikin ɓaraguzan ginin.

Har yanzu dai ba a san dalilin ya janyo rugujewar ginin ba mai shekaru 40 a ranar Alhamis.

An ƙirga cewa akwai mutum 102 a cikin ginin, sai dai babu tabbas ko mutum nawa ne ciki lokacin da ya ruguje. An ceto gwamman daga cikin ɓaraguzan ya zuwa yanzu.

Shugaba Joe Biden ya bai wa hukumar agajin gaggawa ta kasar da ke Florida umarnin ta taimaka da kayan aiki wajen ceto mutanen da ke cikin ginin.

Lokacin da dare ya yi, masu aikin ceton sun yi ta amfani da wasu kananan kyamarori da wasu karnuka da aka bai wa horo wajen aikin ceton mutane.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

"Yan kwana-kkwana da masu aikin ceto na cikin wajen na ci gaba da aiki da karnukansu," in ji shugaban 'yan sanda Freddy Ramirez.

"Suna ta fama da bincike, za kuma su ci gaba da hakan na wani tsawon lokaci. Ba za su tsaya ba. Za su ci gaba da aiki har dare."

Masu binciken sun jiyo wata kara da kuma wasu hayaniya daga nesa, amma dai basa jiyo muryar da za su iya ganewa daga cikin baraguzan.

Masu aikin ceto

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu aikin ceto tare da karensu suna neman masu wadanda ginin ya danne

Amma hukumomi sun ce aikin na tattare da haɗari saboda gine-ginen saman za su iya ƙara rugujewa.

"Akwai hanyoyin da ake bi masu jinkiri amma na kwarai," in ji Ray Jadallah, shugaban hukumar kwana-kwana na Miami. "A duk lokacin da muka fara janye baraguzan kasa na sama za su fara zubowa."

Ruwan saman da ake yi akai-akai da kuma tsawar da ake samu na daga cikin abubuwan da suke kara sanya aikin tsaron yana wahala.

Aerial shot of collapsed block

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani bangare mai girma na ginin mai tsawon hawa 12 ya ruguje a ranar Alhamis.

Tuni hukumomi suka fara daukar samfurin kwayoyin DNA din 'yan uwan wadanda suka ɓata, ko da za a ceto wadanda ba a kai ga ganewa ba.

Yan uwan wadanda suka ɓatan sun yi carko-carko a kusa da inda ginin ya ruguje, suna jiran labarin ƴan uwansu a tsorace.

Nicolas Fernandez ya ce ya kira abar kaunarsa amma ba ta dauka ba.

"Ina ganin sun mutu," ya shaida wa CBS. "Ba wai na yanke kauna ba ne, amma mun ta kiransu ba sa dauka."

People embrace under an umbrella at the Surfside Community Center

Asalin hoton, Reuters

Jenny Urgelles ta tashi da labarin iyayenta na cikin ginin. Ta kira su su duka biyun amma wayoyinsu sun shiga tsarin barin sakon murya.

"Har yanzu ina da fata mai kyau. Na kagu in san me ya faru," ta gaya wa wani gidan talabijin.

Wani da ya rasa nasa iyayen ya ce sun shaida wa ɗan sandan da ya zo wurinsu ya jirasu a ɓangaren gidansu. Daga nan "Sai duka ginin ya tarwatsae cikin wata kara mai kiɗimarwa," in ji Mr Cohen.

Amma daga baya ya yi magana da ma'aikatan agaji kuma sun samu nasarar ceto mahaifinsa daga cikin ginin kan ya gama faduwa.

line

Sharhin wakilin BBC Will Grant daga Miami

Ginin duka ya zama ɓaraguzai bayan rugujewar da ya yi.

Duka kasan ginin ya zabge daga jikin saman: gini mai hawa 12 ya zama ɓaraguzai.

Za ka iya ganin cikin ginin kai tsaye daga waje, ana iya gano dan karamin gida akan samn ruwa. Za ka yi ta gani gadaje a waje, duka abubuwan a waje babu kyan gani.

A gefe kuma guda ga wasu gine-gine da iyalai da yawa suka taro.

Abin tsoron a wajensu shi ne ba su san ko iyalansu na ciki ba ko ba sa ciki.

Saboda daya daga cikinu suna cikin hutu, watakila daga cikin masu hutun a samu wadanda suka mutu.

line

Me ya janyo rugujewar ginin?

Hukumomi sun ce ya zuwa yanzu ba su san dalilin rugujewar ginin ba. Amma za a gudanar da bincike da zarar an gama ceto mutane.

Ginin da aka yi tun shkearar 1980 dama ya cancanci a sabunta shi bayan shekaru 40. Masu ginin za su nemi sabbin takardun sabunta gini.

"Akwai maganar yadda ake so gini ya kasance," in ji Magajiyar garin Miami-dade Daniella Levine.

Composite image, comparing before and after part of the building in Surfside, Florida collapsed

An fara aiki game da saman rufin ginin, amma da yawa na ganin wannan ba wani dalili ba ne da zai iya janyo rugujewar ginin.

Kwararrun da suka ziyarci wajen a bara sun ce dama ginin bai wani zauna ba, kuma ya nuna alamun lalacewa tun shekarun 1990.

Map of Miami