Super Eagles: Buhari ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Najeriya da gidaje

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da ba wa tsofaffin ƴan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagles da suka lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika ta 1994 kyautar gidaje masu dakuna uku-uku.

Shugaban ya ce ya cika alkawarin da ya yi wa ƴan wasan ne saboda yadda suka jajirce a gasar da aka yi a Tunusia.

A cewarsa ''Wadannan ƴan wasa sun fito da darajar Najeriya, kuma sun sa muna alfahari da ƙasarmu, don haka abun da za mu yi musu kawai shine cika alkawarin da muka yi musu''

Za a ba su gidajen ne a jihohin da suka zaɓa.

Tuni dai wasu yan Najeriya suka fara mayar da mabanbanta ra'ayi game da tagomashin inda wasu ke yabawa da yunkurin shugaban ƙasar yayin da wasu kuma suke ganin matakin nasa ya zo a makare kuma ba shi ne abubuwan da yan ƙasar suke son gani ba.