Matalautan ƙasashe na fuskantar ƙarancin alluran riga-kafin Covid-19 - WHO

An wallafa

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da cewa yawancin kasashe marasa galihu da su ka dogara kan shirin nan na Covax da ake rarraba mu su alluran riga-kafin kyauta na fuskantar karancinsu domin ci gaaba da kulawa da al'umominsu.

Babban jami'in hukumar mai sun Dr. Bruce Aylward ya ce kawo yanzu shirin na Covax ya samar wa kasashe 131 allurai miliyan 90 ne.

Sai dai ya ce wadannan allurn ba za su kai ko ina ba ganin yadda annobar ke ci gaba da yaduwa.

Wannan koma bayan ya bayyana ne yayin da kasashen Afirka ke fuskantar zagaye na uku na annobar korona.

Ranar Litinin, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su daina handame alluran riga-kafin da su ke yi.

Allurai miliyan 40 ne kacal aka raba wa nahiyar Afirka - wanda kasa da kashi 2 cikin 100 na yawan al'ummar nahiyar ke nan.

An dai kirkiri shirin na Covax ne a bara domin a tabbatar da dukkan kasashen duniya sun sami alluran riga-kafin, ta hanyar kasashe masu arziki za su tallafa wa kananan kasashe.

Kungiyar kasashe bakwai mafi karfin tattalin arziki wato G7 ta yi alkawarin tallafawa kasashen da ba su karfi alluran riga-kafin na korona guda biliyan daya cikin wannan shekarar.

Masana a fannin kiwon lafiya na ganin za a shafe watanni - ko ma shekaru - kafin a iya samar da allura riga-kafin da za su ishi al'umomin duniya.