Usain Bolt: Budurwar fitaccen ɗan wasan tsere ta haifi tagwaye da aka raɗa wa suna Thunder da Saint Leo

Usain Bolt

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ya sanar da haihuwar ce Ranar Mahaifi ta Duniya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Zakaran wasannin Olympic Usain Bolt ya haifi tagwaye da aka rada wa suna Thunder Bolt da Saint Leo Bolt, wato Tsawa da Waliyyi Leo.

Bolt, mai shekara 34, ya sanar da haihuwar a shafinsa na Instagram sa Ranar Mahaifa ta Duniya, inda ya sanya alamar fitila mai haske a kusa da 'ya'yan nasa.

Zakaran na wasannin Olympic ya wallafa hotonsa da na abokiyar zamansa Kasi Bennett, tare da tagwayen maza da kuma 'yarsu mai shekara daya mai suna Olympia Lightning.

Abokan zaman biyu ba su fadi ranar da suka haifi 'yan tagwayen ba.

Kazalika Bennett ta wallafa hoto tare da tagwayen, tana mai cewa Bolt "mutum ne da ke tsayin daka kan iyalansa kuma mahaifin 'ya'yanmu".

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

1px transparent line

An haifi Olympia Lightning a watan Mayun 2020, kuma an sanar da sunanta a bainar jama'a watanni biyu bayan haihuwarta.

Kafin haihuwarta, Bolt ya rika sanar da mabiyansa akai-akai game da halin da cikin Bennett yake ciki. Amma tsakaninsa da Bennett babu wanda ya wallafa komai lkacin da take dauke da cikin tagwayen.

Bolt, dan kasar Jamaica da ke sana'ar tsere, ya yi ritaya a 2017 kuma har yanzu shi ne zakaran tsere ajin mita 100 da mita 200, abin da ya sa ya zama mutumin da ya fi kowa gudu a tarihi.

Bayan ya yi ritaya daga tsere, ya yi yunkurin shiga sana'ar kwallon kafa, amma a shekarar 2019 ya sanar da cewa ya bar harkokin wasa kwata-kwata.

Bolt ba shi ne shahararren mutum na farko da ya sanya wa 'ya'yansa sunaye irin wadannan ba.

A 2013 Kanye West da matarsa Kim Kardashian West, wadanda yanzu aurensu ya rabu, sun ja hankalin duniya lokacin da suka rada wa dansu suna North West, wato Arewacin Yamma.

Shi ma mawaki Jermaine Jackson ya rada wa dansa, wanda yanzu shekarunsa 20, suna Jermajesty.

Bayanan bidiyo, Har yanzu Usain Bolt ne zakaran tsere ajin mita 100 da mita 200