Tallafin ƙasashen waje: Wadanne kasashe matakin da Birtaniya ta dauka na rage tallafi zai fi shafa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Reality Check team
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Ce-ce-ku-ce na daɗa ƙaruwa a kan matakin Birtaniya na zaftare tallafin da take ba wa ƙasashen waje, inda adawa da matakin ke ƙaruwa a tsakanin ƴan majalisar dokoin ƙasar gabanin ƙuri'ar da za a kaɗa a kan batun.
An rage kasafin tallafin na shekara da kaso 0.5 daga yadda yake a baya wato kashi 0.7, sai dai tuni masu adawa da matakin suka soma tutsu, tare da yin kiran a janye matakin.
To shin a kan wa wannan mataki zai ƙare ne? Sannan wa abin zai fi shafa?
Nawa Birtaniya take kashewa wajen tallafawa ƙasashen duniya?
Kason da kasar ke warewa wajen tallafa ƙasashe ya riƙa ƙaruwa a shekarun da suka gabata, daidai da aniyar cimma kashe kaso 0.7 na daga abin da ake samu na kuɗaɗen shiga na cikin gida wato (GNI) a takaice.
Alƙawarin cimma wannan kaso da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya ya samo asali ne tun shekarun 1970, halisalima yana nan ƙunshe cikin dokar majalisar da aka samar a shekarar 2015.

A shekarar da ta gabata, yawan kudin da aka kashe wajen tallafawa ƙasashen waje ya yi kasa a karon farko cikin kimanin shekaru goma, duk da cewa ya cimma kashi 0.7 saboda tattalin arzikin duniya girgiza saboda annobar da ta ɓullo.
A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, gwamnati ta sanar a wani bangare na binciken kashe kudade cewa za ta rage tallafin zuwa kashi 0.5 saboda mawuyacin halin da tattalin arziki ya shiga.
Ministan Kuɗi na Burtaniya Rishi Sunak ya ce "Nufinmu shi ne mu koma zuwa 0.7 lokacin da yanayin kasafin kudi ya bayar da dama."
Ta yaya za a kwatanta Birtaniya da sauran masu bayar da tallafi?
Gwamnatin ta ce har yanzu Birtaniya ta kasance daya daga cikin manyan kasashe masu ba da tallafi a duniya.
Kafin zaftarewar da ta yi. tana bada gudummawa mafi yawa a mataki na biyu cikin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya wato G7.

Wasu kasashen da dama sun wuce kason taimakon da Majalisar Dinkin Duniya ta sa a gaba na 0.7 a 2020, ciki har da Denmark mai kaso (0.73), da Norway mai kaso (1.11) da Sweden mai maso (1.14).
Kuma yayin da Birtaniya ke neman rage kudaden zuwa kashi 0.5, wasu kasashen da suka ci gaba sun yi alkawarin kara yawan kudaden.
Faransa ta sadaukar da gudummawar 0.7 nan da shekarar 2025, kuma Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da shawarar a kara yawan taimakon da Amurka ke bawa kasashen waje.
Wani ɗan majalisa David Davis ya shaida wa BBC cewa: "Ba mu da karfin jagoranci a yanzu, hasali ma muna jefar da ikon da muke da shi ne musamman a Afrika''.
Ina tallafin kasashen waje ke zuwa ?

Tallafin na Birtaniya na taimakawa wajen gudanar da ɗaruruwan ayyuka daban-daban a duniya.
Yawancin kashe kuɗi a cikin 2020 fiye da kashi 55 ya kasance ne a kan taimakon ƙasashe a yankin Afirka wanda aka keɓe don gudanar da wasu ayyuka ko shirye shirye.
Kashi 39 ne kawai na kudaden aka kashe wajen taimakawa kasashen yankin Asiya, yayin da sauran suka tafi wasu kasashe na fadin duniya.
Sannan yawancin kudin na tafiya wajen ayyukan haɓaka abubuwan more rayuwa da kuma kawo karshen matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita.
Alkalumman da gwamnati ta fitar a shekarar 2019 sun nuna cewa Pakistan ce kan gaba a wannan shekarar wajen samun tallafin kasashen wajen sai kuma kasashen Habasha, da Afghanistan, da Yemen, da Najeriya, da Bangladesh da Syria.

Asalin hoton, Getty Images
Hakanan ana ba da wasu kuɗaɗen Birtaniya ga hukumomin duniya kamar na Majalisar Dinkin Duniya da sauransu don kashewa yadda suka ga dama, wannan taimako ne na bangarori da yawa.
A cikin 'yan shekarun nan, yawancin taimakon da Birtaniya ke bayarwa ya kasance na bangarori biyu ne, kusan kashi biyu bisa uku, maimakon masu yawa.
Menene tasirin yankan?
Wannan yana da wahalar tantancewa a halin yanzu saboda ba a samar da cikakken bayani game da takamaiman ragin kudade ba.
Ko yaya, wasu kungiyoyin agaji gami da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya tuni suka yi magana game da mummunan tasirin da hakan ke haifarwa.
Hukumar kula da tsarin iyali ta Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) tana shirin rasa kashi 85% na kudaden ta daga Burtaniya, ragin kusan £ Miliyan130 ko Dala Miliyan (184).
Cikin wata sanarwa UNFPA ta ce, "Wannan ragin zai kasance mai cutarwa ga mata da 'yan mata da dangoginsu a dunk fadin duniya."
Shima asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) zai ga an rage kudaden da ke bashi da kusan kashi 60%.

Asalin hoton, Unicef/Naftalin
Ana sa ran tallafin da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ke samu daga Birtaniyan shima zai ragu da kusan kashi 80 cikin 100.
"Tallafin na taimakawa wajen karfafawa mata matasa da 'yan mata matasa da kuma samun damar yin jima'i ba tare da gamuwa da kowacce irin illa ba, da haihuwar mata lafiya da kuma tabbatar da kare yancinsu a duk duniya, musamman ma Afirka," in ji hukumar.
Kungiyar yaki da cutar shan inna ta Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ma za ta za ta rasa kusan dukkanin kudaden da take samu daga Burtaniya, in ji hukumar a cikin wata sanarwar da ta fitar.
Kungiyar ta ce Birtaniya ce ta biyu a jerin masu ba ta tallafi, kuma kudaden za su ragu daga £ Miliyan 110 zuwa E Miliyan 5 kacal a bana.
Wanne tasiri hakan zai yi ga wasu ƙasashe ?.
Kwamitin Ceto na Kasa da Kasa (IRC) ya ce lamarin ya yi matukar shafar aikinsa a Siriya, domin an rage kusan kashi 75 cikin 100 na kudaden da yake samu daga bara zuwa yanzu.
A Yemen, wadda ake dauka a matsayin mafi fama da mummunan bala'i a duniya, kudin tallafin da Birtaniya ke bayarwa na agaji ya yi kasa zuwa £ Miliyan 87.2 daga £ Milyan 139.1m da aka yi alkawari a shekarar 2020.
A Pakistan, yawancin kudin ana kashe su ne kan shirye-shiryen rage talauci, da inganta ilimi, da kula da albarkatun ruwa, da kuma inganta kiwon lafiya da sauran ayyukan jin kai.
A cewar kungiyar agaji ta kasa da kasa (IRC), ragin zai yi tasiri ga ilimi a yankunan karkara na Pakistan.
Babban daraktan kasar na IRC, Adnan Junaid, a kwanan nan ya ce dole ne su dakatar da shirin karatunsu a watan Maris kuma "suna nan suna jiran jin ko kashi na biyu na kudin zai zo ko a'a".
Kusan 'yan mata 11,000 a yankunan karkara na Pakistan ba za su iya zuwa makaranta ba idan aka dakatar da ba da tallafin, in ji IRC.
A cikin wata wasika da BBC ta samu, kungiyoyi masu zaman kansu guda takwas wadanda ke ba da kayan agaji ga 'yan gudun hijirar Rohingya dake Bangladesh sun rubuta wa gwamnatin Burtaniya bukatar neman a sauya shawarar.

Asalin hoton, Getty Images
Tallafin da Birtaniya ke bai wa Habasha galibi na tallafawa shirye-shiryen rage talauci, da kiwon lafiya, da tsarin iyali ciki har da samar da magungunan hana haihuwa, da tallafawa 'yan gudun hijira da bakin haure, da ilimi da samar da tsaftatacceb ruwa da tsaftar muhalli.
A Najeriya, kudaden na zuwa ga ayyukan da suka hada da hada-hadar kudi, da abinci, da ilimi, da kiwon lafiya, da makamashin hasken rana ga makarantu da asibitoci, da ayyukan zabe da kungiyoyin farar hula.
Wata kungiya a Najeriyar mai suna Women for Women International ta ce Birtaniya ta kawo karshen yarjejeniyar ba da tallafi na shekaru uku da ita wadda aka fara biyan kudin rabi da rabi.
"Ban taba cin karo da yanayin da mai bayar da ya fasa cika alkawarin da ya dauka ta bangare daya ba," in ji Bukola Onyishi, manajar kungiyar.
Ita ma wata kungiya mai suna Farm Africa na gudanar da wani shiri na taimakawa mata makiyaya a kasashen Yuganda da Habasha wajen samar musu da wuraren kiwon awaki domin inganta abinci mai gina jiki, sai dai a yanzu aikinta zai zo ƙarshe bayan ta kudade.
Me gwamnati ta ce?
Sanarwar da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Dominic Raab ya fitar a cikin watan Afrilu ya yi bayanin abubuwan da suka fi fifiko ga sashensa, kasancewar kaso 80 cikin 100 na talalfin da ƙasar ke bawa kasashen waje na fitowa ne daga ma'aikatarsa, wadanda suka hada na shirin magance matsalar sauyin yanayi da kuma yaki da annobar korona da ma aniyar inganta ilimin 'ya'ya mata.
Ya kuma ce Birtaniya ta kasance ta uku daga cikin masu bayar da tallafi ta fuskar yawan kudaden shigarta, amma bai yi tsokaci a kan batun rage tallafin ba.
Wasu bayanan sirri da aka kwarmata a watan Afrilu, sun bayyana damuwar gwamnati kan yadda ta dauki matakin rage kudaden da atake bawa kasashen waje da ta dauka.
Gwamnatin ta kuma kare matakin a matsayin "matakin wucin gadi" bisa hujjar cewa a daidai lokacin da ake fama da matsalar tattalin arziki, masu jefa kuri'a a Burtaniya za su yi tsammanin za a ba da fifiko wajen gudanar da ayyukan cikin gida.
Bincike da shafin YouGov ya yi a watan Nuwamban da ya gabata a daidai lokacin da aka fitar da sanarwar rage kudaden ya nuna cewa kashi biyu bisa uku na al'umar Burtaniya sun goyi bayan rage kashe kudade kan tallafin kasashen waje.
Wani binciken da aka gudanar a wannan watan na Fabrairu ya nuna sama da kashi 70 cikin 100 na 'yan Birtaniyya sun yi imanin cewa ya kamata a dakatar ko a rage kudaden saboda tasirin cutar krona ga tattalin arzikin kasar.











