Da gaske suna linzami ne kamar yadda Hausawa kan ce?

Name badges

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Christian Jarrett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa

Wataƙila za ku iya samun ci gaba ta hanyoyi da dama da iyayenku suka tsara - tun daga ƙaunarsu da karamcinsu.

Amma kuma ƙila ba tunanin tasirin wani muhimmiyar kyauta ba da suka ba ku ba - sunanku - ko kuna so da kuma yadda jama'a suka ɗauka.

Iyaye sukan shiga tunani da zullumi kan sunan da za su kira ƴaƴansu. Wani lokaci yakan iya zama zakaran gwajin dafi da kuma nuna ƙwarewa domin bayyana martabarsu ko asalin daga zuriya.

Amma wani abu da iyaye ba su fahimta ba - ni ma ban sani ba - shi ne zaɓin suna da suke yi wa ƴaƴansu na iya tasiri ga yadda sauran yara ke kallonsu da kuma yadda ƴaƴansu za su kasance.

"Saboda ana amfani da suna a tantance mutum da kuma yin mu'amula da shi a kullum, domin wannan na iya zama tushen tunanin mutum da kuma alaƙarsa da mutane," in ji David Zhu, masanin halayyar ɗan Adam a jami'ar Arizona da ke binciken ilimi kan sunaye.

Tabbas, abubuwa da yawa suna tasiri ga halayenmu. Wasu daga ciki suna tasiri ne daga kwayoyin halittarmui, haka ma mutanen da muke tarayya da su da rawar da muke taka wa a rayuwarmu, ko dai a wurin aiki ko a tsakanin iyali.

Duk da waɗannan, abu ne mai sauƙi mu manta rawar da suke taka wa ga sunayenmu - wani babban tasiri a tattare da mu tun daga haihuwa kuma yake ci gaba da kasancewa da mu a rayuwa (idan har ba mu sauya ba.)

Kamar yadda Gordon Allport, ɗaya daga cikin masanan halayyar ɗan Adam a 1961, "babban muhimmin abin da zai ci gaba da kasancewa da mu a rayuwarmu shi ne sunanmu."

Baby with name tag on wrist

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Galibin mutane suna ci gaba da amfani da sunayen da aka sanya musu lokacin da aka haife su, ko da yake wasu sukan sauya sunayen idan sun girma

A mataki na farko, sunanmu kan yi cikakken bayani kan ƙabila da kuma asalinmu, inda a wannan duniyar ta nuna bambanci zamantakewa.

Misali kamar binciken da aka gudanar bayan harin 9/11 ya gano cewa mutum na iya rasa aiki idan har sunansa ya yi kama da na larabawa idan aka kwatanta da irin na farar fata.

Wannan a mafi yawancin lokuta, musamman saboda suna kan kasance babbar manuniya ga asali.

Wannan bai kamata a ɗauki shi da wasa ba, amma ba a nan ba ne tasirin suna ya ƙare.

Sunaye kan iya zama gama-gari kuma suna iya tasiri mai kyau da marar kyau ta fuskar ma'ana, za su iya jan hankali kuma abin ƙyama.

Halayen sunayenmu kan iya tasiri kan yadda wasu za su ɗauke mu da kuma yadda muke ɗaukar kanmu.

Wani bincike da aka gudanar a 2000 da masanin halayyar ɗan Adam na Amurka Jean Twenge ya gudanar, ya gano cewa ko bayan magance tasirin asali da kuma rashin gamsuwa na rayuwa, mutanen da ba su ƙaunar sunansu zai shafi tunaninsu.

Wannan wataƙila ko dai saboda rashin ƙarfin gwiwa da girman kai ya sa ba su ƙaunar sunan ko kuma rashin son sunan shi ya haifar da rashin ƙarfin gwiwa - "suna wata alama ce ta mutum", kamar yadda wata marubuciya Twenge ta bayyana.

Game da yadda suna ke tasiri da yadda muke mu'amula da mutane, za a iya la'akari da wani binciken da aka wallafa a 2011, inda aka tambayi wasu masu amfani da shafin sadarwa cewa ko za su iya mu'amula la'akari da sunayensu.

Jochen Gebauer, wanda yanzu ke a Jami'ar Universität Mannheim, da abokan aikinsa, ciki har da Wiebke Neberich, sun gano cewa mutanen da ke da sunaye da ake ganin ba su dace ba a lokacin (kamar su Kevin) ana iya ƙin yarda da su, idan aka kwatanta su da mutanen da ke da sunaye na zamani (kamar Alexander).

Tabbas, sabon binciken, wanda aka gudanar a Jamus, ya gano cewa mahalarta ba za su iya taimakawa wani baƙo da ke da wani sunan da bai dace ba (Cindy da Chantal su ne sunayen biyu da suka fi samun tsokaci marar kyau) idan aka kwatanta da baƙi da ke da sunayen da aka ƙididdige su. (Sophie da Marie su ne aka fi darajawa da kimantawa).

Sunayenmu na iya samun wannan sakamakon saboda suna iya shafar yadda muke ji game da kanmu da yadda wasu suke mu'amula da mu.

Named mugs for sale on a shop shelf

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sunayen da ake sanya wa wasu abubuwa kan daina zama abubuwan yayi

Bugu da ƙari, yayin da sunan da bai yi fice ba na iya zama mara amfani a gajeren lokaci (zai ƙara hatsarin rashin karbuwa da rage farin jini)

*Christian Jarrettmarubuciyyar kimiya ce kuma marubuciyar littafin Be Who You Want: Unlocking The Science of Personality Change