Fitattun hotunan Afirka: daga 7 zuwa 13 ga watan Mayun shekarar 2021

An wallafa

Mun zabo muku fitattun hotunan Afirka na wannan makon:

Wasu yara a garin Tarfaya na kudancin kasar Morocco na daukar darasin wasan zamiya a kyauta ranar Talata

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu yara a garin Tarfaya na kudancin kasar Morocco na daukar darasin wasan zamiya a kyauta ranar Talata
Muslim worshippers are seen through triangle-shaped recess windows.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Jumma'a a kasar Senegal, Musulmai na gudanar da sallah a Masallacin Divinity a Dakar babban birnin kasar.
Ranar Laraba a birnin Abidjan, kasar Ivory Coast, wannan yarinyar na cikin Musulman da suka yi bikin sallar kawo karshen azumin watan Ramadan.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Laraba a birnin Abidjan, kasar Ivory Coast, wannan yarinyar na cikin Musulman da suka yi bikin karamar sallar bayan kawo karshen azumin watan Ramadan.
1px transparent line
Washegari a birnin Nairobi na kasar Kenya, nan ma Musulmai sun gudanar da bikin Karamar Sallah…

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Washegari a birnin Nairobi na kasar Kenya, nan ma Musulmai sun gudanar da bikin Karamar Sallah…
Bayan sallar asubahi an fara yin zanen adon lalle….

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bayan sallar asubahi an fara yin zanen adon lalle….
Kwanaki kadan kafin karamar sallah, an hango wannan yaron a birnin Alkahira na kasar Masar lokacin sallar Magriba a masallacin Amr Ibn El-Aas.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kwanaki kadan kafin karamar sallah, an hango wannan yaron a birnin Alkahira na kasar Masar lokacin sallar Magriba a masallacin Amr Ibn El-Aas.
A ranar Alhamis, Musulmai a Masallacin Tafara Jamat a babban birnin kasar Zimbabwe na cin dabino da a al'adance a ke fara yin buda-baki da shi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Alhamis, Musulmai a Masallacin Tafara Jamat a babban birnin kasar Zimbabwe na cin dabino da a al'adance ake fara yin buda-baki da shi.
Wani mai aikin sa-kai na waucewa ta tsakanin jerin kwalaben ruwan sha a dandanlin Meskel a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia, kafin taruwar dubban Musulmai don yin buda-baki - na azumin watan Ramadan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai aikin sa-kai na waucewa ta tsakanin jerin kwalaben ruwan sha a dandanlin Meskel a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia, kafin taruwar dubban Musulmai don yin buda-baki - na azumin watan Ramadan.
A ranar Litinin a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, wani mutum dauke da bulon siminti a harabar wata masana'antar buga bulo.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, wani mutum dauke da bulon siminti a harabar wata masana'antar buga bulo.
Ranar Lahadi, Souleymane Cissokho, dan asalin kasar Senegal yana murnar galabar da ya samu a kan abokin karawarsa Kieron Conway a gasar wasan kokawa a jihar Texas ta Amurka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Lahadi, Souleymane Cissokho, dan asalin kasar Senegal yana murnar yn nasara a kan abokin karawarsa Kieron Conway a gasar wasan kokawa a jihar Texas ta Amurka.
Wani gunkin Persephone na Karni na Biyu da aka mika wa ofishin huddar jakadancin kasar Libya a London babban birnin kasar Birtaniya. An kwace wannan sassakakken gunkin daga wurin ajiyar kayan tarihi da Majalisar Dinkin Duniya ke karewa, wanda daga bisani aka yi fasa-kwaurinsa zuwa kasar ta Birtaniya inda 'yansandan kan iyaka suka kwace.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani gunkin Persephone na Karni na Biyu da aka mika wa ofishin huddar jakadancin kasar Libya a London babban birnin kasar Birtaniya. An kwace wannan sassakakken gunkin daga wurin ajiyar kayan tarihi da Majalisar Dinkin Duniya ke karewa, wanda daga bisani aka yi fasa-kwaurinsa zuwa kasar ta Birtaniya inda 'yan sandan kan iyaka suka kwace.
A ranar Asabar, yara na wasan ninkaya a wajen birnin Alkahira ...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar, yara suna wasan ninkaya a wajen birnin Alkahira ...
1px transparent line
Yara da dama na wasa ninkaya don sanyaya jikinsu a cikin kogin Nilu yayin da ake zabga zafi.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yara da dama na wasa ninkaya don sanyaya jikinsu a cikin kogin Nilu yayin da ake zabga zafi.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.