Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Hotunan da ke nuna yadda tashin hankalin ya ƙazanta
Tashin hankalin da ke aukuwa a yankuna Falasdinu da kuma Isra'ila sai karuwa yake yi, inda rokoki ke afkawa cikin biranen Isra'ila babu kakkautawa, su kuma su na kai nasu hare-haren a Gaza, ban da tarzomar da ta barke a biranen Isra'ilar tsakanin Larabawa da Yahudawan kasar.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza wadda ke karkashin ikon Hamas ta ce mutum 83 ne hare-haren da Isra'ila ke kai wa su ka rasa rayukansu, kuma fiye da mutum 480 sun sami raunuka. A kalla kananan yara 17 aka halaka cikin 83 da aka bayyana a baya.
Yayin da ake jimamin wannan halin a Gaza, ma'aikatan kiwon lafiya na Isra'ila sun ce hare-haren roka da Hamas ke kai wa cikin kasar daga Gaza sun hallaka mutum bakwai, ciki har da kananan yara biyu.
Rikici ya kuma barke tsakanin al'umomin Larabawa da Yahudawa cikin Isra'ila.
Rikicin ya barke ne ranar Litinin bayan an shafe makonni ana zaman doya da manja a Birnin Kudus ta Gabas, lamarin da ya haifar da rikicn da aka yi a masallacin Kudus.
Wadannan hotunan na bayyana halin da ake ciki a rikicin na baya-bayan nan.