Bayanan hoto, Wani bene ya kama da wuta a Gaza bayan da Isra'ila ta kai ma sa hari da jiragen sama na yaki ranar Alhamis 13 ga watan Mayu
An wallafa
Tashin hankalin da ke aukuwa a yankuna Falasdinu da kuma Isra'ila sai karuwa yake yi, inda rokoki ke afkawa cikin biranen Isra'ila babu kakkautawa, su kuma su na kai nasu hare-haren a Gaza, ban da tarzomar da ta barke a biranen Isra'ilar tsakanin Larabawa da Yahudawan kasar.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza wadda ke karkashin ikon Hamas ta ce mutum 83 ne hare-haren da Isra'ila ke kai wa su ka rasa rayukansu, kuma fiye da mutum 480 sun sami raunuka. A kalla kananan yara 17 aka halaka cikin 83 da aka bayyana a baya.
Yayin da ake jimamin wannan halin a Gaza, ma'aikatan kiwon lafiya na Isra'ila sun ce hare-haren roka da Hamas ke kai wa cikin kasar daga Gaza sun hallaka mutum bakwai, ciki har da kananan yara biyu.
Rikici ya kuma barke tsakanin al'umomin Larabawa da Yahudawa cikin Isra'ila.
Rikicin ya barke ne ranar Litinin bayan an shafe makonni ana zaman doya da manja a Birnin Kudus ta Gabas, lamarin da ya haifar da rikicn da aka yi a masallacin Kudus.
Wadannan hotunan na bayyana halin da ake ciki a rikicin na baya-bayan nan.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Yawancin mace-macen sun auku ne a Gaza, yankin da Isra'ila ta sa a gaba a harin da ta ke yi daga sama
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan harin an kai shi ne kan ginin Al-Walid da sanyin safiyar Alhamis
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya na Falasdinu sun ce an kashe kananan yara saboda hare-haren na Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Falasdinawa masu yawa sun fice daga unguwanninsu zuwa yankuna da su ka fi zaman lafiya
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Isra'ila ta ce hare-haren da ta ke kai wa ta sama martani ne kan harin rokar da ake kai wa kan biranenta
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Birnin Ashkelon da ke kudancin Isra'ila ya fi shan wuya daga hare-haren da mayakan Falasdinu ke kai wa da rokoki daga Gaza
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Isra'ila na iya kakkabo yawancin rokokin da wata na'ura mai suna Iron Dome
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Sai dai karar jiniya da ake kunnawa gabanin isowar rokokin na sa miliyoyin 'yan Isra'ila tserewa zuwa neman mafaka, inji dakarun tsaron Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Zanga-zangar da ake yi bisa titunan Isra'ila sun rikide zuwa tarzoma da hare-hare...
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, kuma jami'an tsaro na mayar da martani da karfin ikonsu - a nan ga wani dan sanda na jefa nakiya mai fashewa domin razana Falasdinawa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yadda ta kasance ke nan ranar Alhamis a birnin Hebron
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Garuruwa masu dama a Isra'ila sun fuskanci rikici tsakanin Yahudawa da Larabawa - wannan shagon sayar da abinci ne mallakin wani Bayahude a Acre da aka kai wa hari.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, inda matukin wannan motar kuwa an ciro shi dag cikinta ne aka lakada ma sa duka a garin Bat Yam
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Isra'ila ta fara aikawa da dubban sojojinta zuwa kan iyakarta da Gaza, kuam ta yi gargadin za ta iya kutsawa cikin yankin