Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Keita, Bertrand, Llorente, Andersen, De Paul, Ings, Patricio, Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images
Mahaifiyar dan wasa Cristiano Ronaldo wato Dolores Aveiro, na son dan ta koma murza leda a Lisbon, idan dan wasan mai shekara 36 ya bar kungiyar Juventus a lokacin bazara. (Guardian)
Kungiyar Tottenham na fatan za ta gamsar da dan wasan tsakiya na Denmark mai shekara 24 Joachim Andersen, wanda aka bai wa kungiyar Fulham shi aro, da ya shiga kungiyar domin fafatawa da babbar kishiyasu wato Arsenal. (BT via TeamTalk)
Tsohon dan wasan tsakiya na Xavi, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi domin ci gaba da zama a kungiyar kwallon kafa ta Qatar wato Al-Sadd har zuwa shekarar 2023, hakan abin kunya ne ga shugaban Barcelona Joan Laporta, wanda ke neman hanyar maye gurbin mai horas da 'yan wasa na yanzu Ronald Koeman. (Mail)
Wolves's mai tsaron ragar kungiyar Portugal Rui Patricio, mai shekara 33, wanda shekara daya ta rage masa ya kammala kwantiraginsa da Molineux, ta yiwu sabon manajan Roma Jose Mourinho ya dauke shi. (Calciomercato - in Italian.
Ian Wright bai taba tsammanin dan wasan tsakiya na Arsenal Dani Ceballo mai shekara 24 zai iya koma kungiyar Real Madrid baki daya ba. (Metro)
Leeds United ta sha gaban AC Milan a kokarin rattaba hannu kan jarjejeniyar daukar dan wasan tsakiya na Liverpool Rodrigo De Paul, mai shekara 23, sai dai ita kan ta Liverpool na nuna sha'awar dauko dan wasan Argentina. (Il Milanista - in Italian)
An fahimci cewa Manchester United na shirin ware kudi fam miliyan 68, domin dauko dan wasan tsakiya na Atletico MadridMarcos Llorente, da ake sa ran matshin mai shekara 26 zai yi rawar gani a gasar with the La Liga.(Mirror)
Leicester City na sha'awar rattaba hannu domin dauko dan wasan Southampton Ryan Bertrand. Kwantiragin dan wasan mai shekara 31 zai kare a karshen kakar wasan bana, bayan shafe shekara bakwai a kungiyar.(Leicester Mercury)
RB Leipzig ta Faransa na son dauko dan wasan tsakiya Dayot Upamecano, mai sheakru 22, wanda zai shiga gasar Bundesliga da za su kara da Bayern Munich kan kudi fam miliyan 38, asai dai da alama bai amince da hakan ba, domin ya taba watsi da tayin da Manchester United a lokacin ya na da shekara 17. (The Athletic - subscription needed)











