Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Bala Ahmed
Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Muhammad Bala Ahmed a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:
Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya zo muku da Sheikh Muhammad Bala Ahmed, malamin addinin Musulunci da ke Bauchi.
An haifi Sheikh Muhammad Bala Ahmed a watan Junairun 1950 a garin Bauchi na jihar Bauchi da ke Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.
Sunan mahaifinsa Malam Ahmad Mahmoud Baban Inna, mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Fatima.
Bayan ya isa yaye sai kakanshi Malam Mahmoud Muhammad Bello limamin Bauchi na wancan lokacin, ya dauke shi, ya taso a hannunsa inda ya yi karatun AlKur'ani da sauran litattafai har zuwa shekarar 1966.
Malamin ya shaida wa BBC cewa a ba tare da son kakansa ba ya tafi makarantar boko - amma abokan mahaifinsa ne suka ga dacewar haka suka tsaya aka sanya shi a makarantar mai suna Kofar Nasarawa wadda aka fi sani da Senior Day Secondary School.
Su ne na farko suka fara zama a aji daya, daga aji biyu aka yi masa karin aji, inda aka sanya shi a aji hudu. Amma saboda babu aji hudu sai aka mayar da shi Kobe Primary School, inda ya shekara biyu daga shekarar 1968 zuwa 69.
Daga nan ya yi jarrabawa a makarantar Arabiyya da ke garin Gombe, wato Government Arabic Teachers Collage a shekarar 1970.
Bayan kammala koyarwa a matsayin malamin Arabiyya na shekara biyu, sai aka ba shi malamin aji daga nan kuma ya zama Hedimasta a shekarar 1976 lokacin da ka soma UBE.
Daga bisani ya ga dacewar ya karo ilimi, sai ya tafi Jami'ar Jos ya yi Babbar Difiloma a fannin mulki, ya kuma ci gaba da aiki har ya kai matsayin shugaban ma'aikatar lura da shirye-shiryen aiki da gudanar da su.
Malam Bala Ahmad ya sake komawa Jami'a, amma wannan karon ta Abukatar Tafawa Balewa, inda ya kammala a shekarar 2000.
Daga nan ne, aka ba shi matsayin sakataren karamar hukuma, a kuma dai lokacin ne aka ba shi na'ibin masallacin Bauchi.
Duk da kakansa ya rasu a shekarar 1990 ya ci gaba da karatu a gaban mahaifinsa.
A shekarar 2021 aka tabbatar masa da mukamin limamin Bauchi har zuwa wannan shekara ta 2021.
Don haka sai ya yi ritaya ya mayar da hankali kan aikin limanci.












