KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 7 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Araqchi ya wallafa hoton wasiƙar shugaban Pakistan ga Mojtaba Khamenei

    ....

    Asalin hoton, @s_a_araghchi

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya wallafa hotuna a Telegram daga ganawarsa da Ministan Cikin Gida na Pakistan, Mohsin Naqvi, inda aka nuna shi yana karɓar wata wasiƙa daga shugabannin Pakistan zuwa Mojtaba Khamenei.

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Iran sun bayyana cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan “sabbin matakan diflomasiyya da ke da alaƙa da tattaunawar Iran da Amurka.”

    Ministan harkokin wajen Iran ya ce Mohsin Naqvi ya kai ziyara Tehran ne domin ci gaba da taka rawar sasanci tsakanin Iran da Amurka.

    Bayan ganawarsa da Ministan Cikin Gida na Iran, Eskandar Momeni, Naqvi ya ce ya kawo “wasiƙa ta musamman” da kuma “saƙo mai muhimmanci” daga Asim Munir da firaminista Shahbaz Sharif zuwa ga Mojtaba Khamenei.

    Wannan ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin rage tashe-tashen hankula a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen yankin.

  2. Ko AI zai kori jaruman Kannywood?

    YUSRAH VENTURES FILM PRODUCTION

    Asalin hoton, YUSRAH VENTURES FILM PRODUCTION

    Ana cigaba da tafka muhawara kan yiwuwar amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen shirya fina-finan Hausa, tun bayan da fim mai suna "Dirty Game" da aka yi da Ingilishi amma da zubin Hausa ya fito.

    Fim ne da aka yi kacokam da ƙirƙirarriyar basira ta AI, inda aka ƙirƙiri labarin, sannan aka ƙirƙiri jarumai da murya da sauran abubuwan fim ɗin baki ɗaya.

    An dai daɗe ana fargabar ƙirƙirarriyar basira za ta raba mutane da dama da aikinsu, duk da cewa fasahar ta riga ta zo, kuma tana tattare da alherai da yawa da masana suke bayyanawa.

  3. 'A ranakun wasannin Iran ne tawagar za ta riƙa shiga Amurka'

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Tawagar ƴanƙwallon ƙasar Iran sun isa ƙasar Mexico a daidai lokacin da ake cigaba da tata-ɓurza kan damar shiga Amurka domin taka leda a wasannin gasar cin kofin duniya.

    Dukkan wasannin Iran na rukuni a Amurka ne, amma aka tsara cewa dole ƴanwasan ƙasar su zauna a Mexico, sannan su riƙa tafiya Amurka su buga, sannan su koma Mexico a ranar wasan.

    Iran dai ta ce akwai jami'an tawagarta da ta ce suna da muhimmanci da aka hana bizar zuwa gasar ta duniya, sannan ta zargi Amurka da katsalanda kan harkokin wasanni.

  4. Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen ceto mutanen da aka sace

    Babagana Umara Zulum

    Asalin hoton, Babagana Umara Zulum/Facebook

    Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya, musamman jami'an aikin soji na musamman na Hadin Kai bisa ceto mutum 360 da aka sace a jihar daga tsaunin Mandara.

    Tsaunin Mandara na daga cikin fitattun maɓoyar mayaƙan Boko Haram da ke da tsananin haɗari a kudancin jihar Borno.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya ya fitar, Gwamna Zulum ya bayyana ceto mutanen na Ngoshe a matsayin babbar nasara.

    Ya ce nasarar za ta ƙara taimakawa wajen kwantar da hankalin ƴan ƙasar, musamman ƴan jihar a kan ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da tsaro.

    "Ina godiya ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da babban hafsan tsaron Najeriya da babban hafsan sojin ƙasa da kwamandan sojojin Borno da sojojin baki ɗaya bisa ƙoƙarin da suka yi."

  5. Wace ƙungiya ce ta fi yawan ƴanwasa da za su buga kofin duniya a 2026?

    Wasa

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City tana da ƴan wasa 19 da za su wakilci kasashensu a gasar cin kofin duniya 2026 da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Daga cikin waɗannan ƴan ƙwallon, huɗu suna daga cikin tawagar Ingila da suka haɗa da mai tsaron raga, James Trafford da mai tsaron baya, Marc Guehi da Nico O'Reilly da kuma John Stones da koci, Thomas Tuchel ke fatan za su taka rawar gani.

    Kamar yadda John Stones zai bar Etihad bayan kammala kakar bana, haka shima ƙyaftin ɗin City, Bernardo Silva wanda ya lashe kofuna a ƙungiyar yana kuma ɗaya daga cikin ƴan wasan uku da za su yi wa tawagar Portugal gasar cin kofin duniya tare da Ruben Dias da kuma Matheus Nunes.

  6. NDLEA ta ƙwace kwayoyin tramadol 320,840 tare da kama tsoho a Taraba

    ....

    Asalin hoton, NDLEA/X

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta ce ta gano tare da ƙwace manyan miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye a cikin wata mota da ke ɗauke da kayan gini a jihar Taraba, inda ta gano miyagun ƙwayoyi 320,840 na tramadol tare da wasu magungunan da aka haramta.

    Hukumar ta ce an gano motar ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda jami’anta suka tare ta a Nukkai Timber Shade da ke Jalingo.

    A cikin kayan da aka ƙwato akwai allurai 600 na pentazocine, kwayoyi 4,500 na rohypnol, da kuma kwalaben syrup 299 masu ɗauke da codeine.

    A wani samame daban, hukumar ta kama wani tsoho mai shekara 75 a jihar Ebonyi da ake zargi da sayar da tabar wiwi

    Hukumar ta kuma kama wasu mata da maza a jihohin Edo, Imo, Kano da Gombe kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

    NDLEA ta ce za ta ci gaba da yaki da masu fataucin miyagun ƙwayoyi ba tare da la’akari da shekaru ko jinsi ba.

  7. Mutum ɗaya ya mutu a harin bindiga a tsakiyar Isra’ila

    ‘Yan sandan Isra’ila sun ce mutum ɗaya ya mutu , yayin da wasu biyar suka jikkata a wani harin bindiga da aka kai a garin Kochav Yair da ke tsakiyar ƙasar.

    Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun harbe wanda ake zargi da kai harin, wani ɗan ƙasar Isra’ila daga birnin Tayyiba, wanda ya yi amfani da mota mai lambar Isra’ila wajen kai harin.

    Sojojin Isra’ila sun kuma ce sun rufe wata hanyar shiga yankin Gaɓar Yammacin da Kogin Jordan tare da killace wasu ƙauyuka na Falasɗinawa da ke kusa.

  8. Wane ne Muhammad Minshawi: "makarancin Qur'ani"mai matuƙar alkunya

    ....

    Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي

    "Haske daga haske kuma duniyar da ta fito daga wata babbar duniyar. Ba abin da wani zai ce game da shi face cewar shi dan itace ne mafifici da ya fado daga mafificiya." Da wadannan kalaman ne makarancin kur'anin nan na kasar Masar Marigayi Fatih Al-Maliji ya bayyana dan'uwansa Muhammad Siddiq Al-Minshawi.

    Wannan murya mai dadin sauraro cikin girmamawa, wadda ta shahara a ko'ina cikin kasashen Larabawa da Musulunci, ba wata baiwa ce ta musamman ba a cikin zuri'ar gidan Al-Minshawi. Sheikh Muhammad Siddiq ya fito ne daga cikin tsatson mahaddatan Alkur'ani mai girma, kamar yadda ya fada a wata hira da ya yi da gidan rediyon Masar.

    An bayyana gidan da ya fito a matsayin "Gidan Kur'ani"; Kakansa, Sheikh (Sayyid), da kakansa, (Tayyib) Al-Minshawi, dukkansu suna daga cikin mashahuran masu karatun kur'ani mai tsarki a kasar Masar, amma sun riga sun wuce ba tare da an taskace karatunsu ba, kamar yadda kawunsa (Ahmed Al-Sayyid) Al-Minshawi ya shuɗe.

  9. Gwamnatin Kaduna ta fara horar da dakarun tsaron gandun daji 1,000

    ....

    Asalin hoton, Uba Sani/X

    Gwamnatin jihar Kaduna ta fara horar da dakarun tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kare dazuka da kuma fatattakar masu aikata laifi da ke fakewa a cikin su domin yaƙi da rashin tsaro a jihar.

    An ce dakarun za su rika lura da motsin da ake yi a dazuka, tare da tattara bayanan sirri da taimakawa jami’an tsaro wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

    Gwamna Uba Sani, wanda sakataren ma’aikatar fadar gwamnati ya wakilta, ya buƙaci wadanda ke karbar horon su kasance masu ladabi da kwarewa, yana mai cewa za a tura su yankunan da suka fi fama da matsala bayan kammala horaswar makonni shida.

    Gwamnatin ta ce shirin na daga cikin matakan da ake dauka domin kare rayuka da dukiyoyi, da kuma bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.

  10. Sojojin Najeriya sun ce sun ceto mata da yara 360 da aka sace a Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Hadin Kai sun ceto kimanin mata da yara 360 da '’yan ta’adda' suka sace daga ƙauyen Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, kakakin rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya ce aikin ceton ya gudana ne a ranar 6 ga Yuni, tare da haɗin gwiwar sauran runduna ta Musamman a yankunan da ke kusa da Dutsen Mandara.

    Ya ce sojojin sun gudanar da aikn ne da dabarun da suka rikita sansanonin ’yan ta’adda, wanda hakan ya ba su damar shiga da kuma kuɓutar da mutanen cikin nasara.

    A cewarsa, mutanen da aka ceto an sace su ne a harin da aka kai Ngoshe a ranar 3 ga Maris, 2026.

    Sai dai ya ce an samu asarar rayukan jarirai biyu yayin aikin ceto, sakamakon wahalar hanya da yanayin da aka fuskanta yayin fitar da su zuwa wuri mai aminci.

    Ya ƙara da cewa dukkan waɗanda aka ceto an yi musu gwaje-gwajen lafiya nan take, inda aka kwantar da wasu a Asibitin Gwamnati da ke Gwoza domin ƙarin kulawa, yayin da aka ba su abinci da ruwa kafin a tura su wurin da ake kula da su na wucin gadi.

  11. Ministan harkokin cikin gidan Pakistan ya gana da Araghchi a Tehran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, a birnin Tehran.

    Kafin hakan, a daren Asabar, Naqvi ya kuma gana da takwaransa na Iran, Eskandar Momeni.

    Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce bayan ganawar, Naqvi ya bayyana cewa ya kai ziyara Tehran ne domin isar da wata “wasika ta musamman” da kuma wani “muhimmin sako” daga babban kwamandan rundunar sojin Pakistan da kuma firaministan ƙasar zuwa ga Mojtaba Khamenei.

    Sai dai rahotannin ba su bayyana cikakken abin da sakon ko wasikar suka ƙunsa ba.

  12. Likitoci na fuskantar hare-hare a Najeriya - NARD

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar likitocin Najeriya masu neman ƙwarewa (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 da ta fara aiwatar da tsarin kasa na kare ma’aikatan lafiya daga hare-hare sakamakon ƙaruwar cin zarafi da farmaki da ake kai wa likitoci a faɗin ƙasar.

    Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai bayan kammala babban taronta na yau da kullum da aka gudanar a Kano.

    Haka kuma ta ayyana rikicin kwadago da gwamnati kan wasu bukatu 14 da har yanzu ba a warware ba a bangaren lafiya.

    Shugaban NARD, Mohammad Suleiman, ya ce yawaitar hare-hare da tsoratarwa da cin zarafi da kuma amfani da karfi kan likitoci na barazana ga tsarin kiwon lafiyar Najeriya wanda tuni yake fuskantar ƙalubale.

    Ya bayyana wannan yanayi a matsayin abin takaici kuma mai haɗarin gaske ga ɗorewar tsarin kiwon lafiya a kasar.

    Daga cikin bukatun da ƙungiyar ta gabatar akwai gaggauta bincike, kama da hukunta waɗanda ke kai hare-hare kan ma’aikatan lafiya, tare da kara tsaurara matakan tsaro a asibitoci da wuraren kiwon lafiya.

    NARD ta kuma buƙaci gwamnati ta fara aiwatar da tsarin kariya da martani ga hare-haren da ake kai wa ma’aikatan lafiya tare da fara aiwatar da dokokin da za su magance matsalar cikin kwanaki 21.

    NARD ta yi gargadin cewa idan ba a biya wadannan buƙatu cikin kwanaki 21 ba, ba za ta iya tabbatar da zaman lafiya a harkokin aiki ba, kuma hakan na iya haifar da ƙarin matakan yajin aiki a fadin kasar.

  13. Ba mu ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ba - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty images/Tasnim

    Wani mamba a kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin Iran, Vahid Ahmadi, ya ce babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka, yana mai gargadin cewa akwai yiwuwar ɓarkewar wani sabon yaƙi.

    A wata hira da ya yi da shafin labarai na Fararoo, Ahmadi ya ce abin da ke akwai a yanzu shi ne dakatar da faɗa na wani lokaci, ba cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

    Ya ce Amurka ba ta cimma manufofin da ta sanya a gaba a lokacin yaƙin ba, kuma a yanzu tana ƙoƙarin matsa wa Iran lamba ta fuskar tattalin arziki ta hanyar toshe hanyoyin ruwa.

    Sai dai ya ce wannan mataki ma bai kai ga nasarar da Amurka ke nema ba.

    Ahmadi ya ƙara da cewa akwai yiwuwar sabon rikici ya sake barkewa, yana mai cewa Iran na da wasu sabbin damar da za ta iya amfani da su idan hakan ta faru.

    Har ila yau, ya soki wasu ƙasashen yankin Gulf, yana mai cewa tsawon shekaru sun dogara da Amurka wajen neman kariya.

    A cewarsa, yakin baya-bayan nan ya nuna cewa ba za a iya samun cikakken tsaro ta wannan hanya ba.

  14. Hezbollah ta ce ta kai hare-hare kan wuraren sojojin Isra’ila a Kudancin Lebanon

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari kan wani hedkwatar rundunar sojin Isra’ila da ke birnin Naqoura a kudancin Lebanon da jirage marasa matuƙa nau’in “Ababil”.

    Hezbollah ta kuma yi iƙirarin cewa mayaƙanta sun kai hari kan sojojin Isra’ila a yankin Hadada da ke kudancin kasar da jirage marasa matuka guda biyu.

    Haka kuma ta ce ta harba rokoki da harsasai na manyan bindigogi kan wuraren da ke kusa da sansanin Beaufort Castle.

    A daren jiya, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa cikin sa’o’i 48 da suka gabata ta kai hare-hare 150 a kudancin Lebanon, inda ta ce ta nufi wuraren da ke da alaka da kungiyar Hezbollah.

    A gefe guda kuma, dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kudancin Lebanon sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan wata motar sojojin Lebanon a yankin Nabatieh, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji uku.

  15. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.