Yadda ɗan adam ke rusa wuraren tarihi na duniya a yayin haƙar ma'adanai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Richard Fisher da Javier Hirschfeld
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
- An wallafa
A duk lokacin da muka yi gini kasa domin haƙo ma'adanai, kamar ɗanyen mai ko duwatsu masu daraja, tamkar muna kawar da wani ɓari ne na tarihi.
Kuma waɗannan ma'adanai su ne abin da marubuciya Astra Taylor ta kira 'dunƙulalliyar rayuwa da ta gabata'.
Irin waɗannan abubuwa na ɗaukar miliyoyin shekaru kafin su taru a wuri guda, amma a yanzu ana amfani da na'urori ko nakiyoyi wurin wargaza su cikin 'ƙanƙanin lokaci.
Tun bayan da ɗan adam ya gane cewa akwai arziƙi danƙare a ƙarƙashin ƙasa, yake ta haƙa domin lalubo abin da ke ciki.
Haƙar ma'adanai ta taimaka wajen sauƙaƙa wa duk wasu ɓangarori na rayuwarmu ta wannan zamani, sai dai tasirin da haƙar ke yi ga asalin yadda duniya take ya yi ƙamari.
Idan ka dubi tasirin da wuraren haƙar ma'adanai ke yi ga doron kasa, zai iya sauya tunaninka game da abubuwan da ka mallaka.
Hatta yadda ake isar da wannan bayani - a bayan wannan na'ura da ka ke kallo, abubuwa ne waɗanda a baya suke damfare jikin duwatsu tsawon ɗaruruwan shekaru.
Haka nan kuma yanzu haka a wani wurin irin wannan buƙata ta ƙarin ƙirƙire-ƙirƙire na ƙara ingiza mutane su ci gaba da binciken irin waɗannan ma'adanai da ke ƙarƙashin ƙasa.
Gaba kadan za mu duba tarin hanyoyin da ha'kar ma'adanai ta sauya yanayin doron ƙasa - Idan ma'adanai da muke haƙowa na daga cikin abinda ya sanya duniya a baya ta kasance a kammale, to kuwa abubuwan da muke da su dankare a gidajenmu a yanzu wasu tabbai ne da ke nuna irin raunin da muka yi wa makomarmu.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.









