Wani hamshakin attajiri na neman mutum takwas da za su raka shi duniyar wata

Yusaku Maezawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yusaku Maezawa na gayyatar mutum takwas daga ko ina afadin duniya don su raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa duniyar wata
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wani hamshakin attajiri dan Japan Yusaku Maezawa yana gayyatar mutum takwas daga ko ina afadin duniya don su raka shi wata tafiya da yake son yi zuwa duniyar wata a jirgin SpaceX flight na Elon Musk.

"Ina son mutane daga ko ina su nemi yin wannan rakiya," kamar yadda ya fada a wani bidiyo da ya wallafa a Tuwita, inda ya kuma wallafa adireshin intanet din da za a shiga a nemi aikin rakiyar.

Ya ce shi zai dauki nauyin gaba daya tafiyar, don haka 'yan rakiyar a garabasa za su je.

An sanya lokacin bulaguron mai taken dearMoon, ne a shekarar 2003.

Wadanda za su nemi wanan rakiya na bukatar cika wasu sharuda biyu: sai sun kasance duk abin da suke na taimakon al'umma ne a wani fannin, kuma sai idan suna da burin taimakon sauran abokan tafyar da suke da irin wannan buri, in ji shi.

"Na sayi dukkan tikitin jirgin, don haka zai kasance tafiya ce ta kashin kai," ya kara da cewa.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

Mr Maezawa, hamshakin mai arzikin a fannin kayan kawa, kuma fasihi, a baya ya ce ya shirya gayyatar fasihai don yin tafiyar tare, amma sai aka gyara tsarin ta yadda mutane daga sassan duniya daban-daban za su samu damar bin jirgin.

"Idan kana kallon kanka a matsayin fasihi, to kai fasihi ne," a cewarsa.

A bara, ya kaddamar da wani shiri na neman sabuwar budurwar da za ta raka shi a bulaguron, kafin daga bisani ya fasa saboda tunani daban-daban.

A shekarar 2018, an ambaci Mr Maezawa a matsayin fasinjan farko mai zaman kansa da zai yi zagaye a duniyar wata a jirgin SapceX, na kamfanin Elon Musk.

Ba a bayyana yawan kudin da Mr Maezawa zai biya na tikitin jirgin ba, amma Elon Musk ya ce makudan kudade ne.

Shirin zuwa duniyar wata na 20223 shi ne zai zama na farko da dan adam zai yi tun bayan shekarar 1972.

Bayanan bidiyo, Bidiyo: 'Abin da ya sa na sayi tikitin zuwa duniyar wata'