Kotu ta umarci wani mutum ya biya matarsa kudin ayyukan kula da gida da take yi

Woman cleaning table

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hukunci dai na zuwa ne bayan China ta gabatar da wani sabon kundin doka da zai shafi fararen hula
An wallafa

Wata kotun a Beijing ta umarci wani mutum ya biya matarsa fansar kudaden aikace-aikacen gidan da ta yi masa kan ya sake ta.

Zai biya matar kudi da suka kai yuan 50,000 kwatankwacin dalar Amurka 5,460 na tsawon bautar da ita da ya yi shekara 5.

Wannan shari'a ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta kan kimar aikace-aikacen gida, inda wasu ke cewa kudin da zai biya sun yi matukar yin kadan.

Wannan hukunci dai na zuwa ne bayan China ta gabatar da wani sabon kundin doka da zai shafi fararen hula.

Daga bayanan kotun, mutumin ne ya nemi rabuwa da matarsa wadda ya aura a 2015.

Da farko dai ta amince a rabu, amma daga baya ta nemi a biya ta wasu kudade, saboda mijin nata baya aikin komai a gidan ba kuma ya kula da yaransu da suke da.

An bai wa matar gaskiya hukuncin da kotun da ke yankin Fangshan a birnin Beijing, inda ta umarce shi ya biya ta kudin kasar yuan 2,000 duk wata, sannan kuma zai biya ta yuan 50,000 na ayyukan da ta yi a baya.

Mai shari'ar ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa raba abubuwan da ma'aurata suka mallaka bayan aurensu ya ƙunshi abubuwa ne kamar ƙadarori. "Amma ayyukan gida sai dai a ƙiyasta darajarsa," in ji alƙalain.

An yanke hukuncin ne ta hanyar amfani da wani ƙuduri na kundin tsarin ƙasar, wanda aka fara amfani da shi a bana. A ƙarƙashin dokar, mata ko miji na da damar neman diyya a yayin saki ko kuma idan ayyuka sun masa yawa musamman na reno da kula da dangi da suka manyanta, tare da taimaka wa abokin zama da aiki.

A baya ma'auratan da suka rabu suna iya neman wannan diyya ne kawai idan har dama an taɓa cimma yarjejeniya - abin da ba a faye yi a China ba.

Lamarin ya jawo muhawara sosai a shafukan sada zumunta har da ƙirƙirar masa da maudu'i, sannan an kalle shi a a manhajar Weibo sau fiye da miliyan 570.

Wasu a shafukan sada zumunta na nuna cewa yuan 50,000 a aikin tsawon shekara biyar ya yi kaɗan matuƙa.

Wata marubuciya ta ce: "Na rasa abin faɗa, ana raina aikin gida da matar aure ke yi. Daukar hayar mai reno a Beijing na tsawon shekaru ya fi ƙarfin yuan 50,000,."

Wasu kuma na ganin maza ne ya kamata su dinga yin ayyukan gida ma tun farko.

2px presentational grey line