Tseren dawaki ya sa wani matashi ya shahara a kasar Senegal

Asalin hoton, Reuters
Bayan ya lashe babbar gasar tseren dawaki ta Senegal shekaru biyu da suka wuce, dan tseren dawaki Fallou Diop, wanda yanzu shekarunsa 19, yana fatan cika burinsa na rayuwa a Faransa a shekara mai zuwa.
"Ina son zama gwarzon dan tseren dawaki a wata kasar baya ga kasata," in ji shi.
"A Morocco ko Faransa, ko kuma duk inda ake gasar tseren dawaki."

Asalin hoton, Reuters
Zohra Bensemra, ta kamfanin dillacin labaran Reuters, ta dauki hotunan atisayen Diop.

Asalin hoton, Reuters
Dawakai da jakuna da alfadarai da aka fi amfani da su wajen harkar sufuri, sun kasance wasu muhimman abubuwan rayuwar yau da kullum a kasar Senegal.
Kuma gasar tseren dawaki ta kara bunkasa tare da kasancewa wani abin nishadi da shakatawa a kasar.

Asalin hoton, Reuters
"Manya ne suka koya mana tun muna 'yan kanana," in ji Diop.
"Tun zamanin kakana, danginmu sun kasance masu matukar kaunar dawakai, bayan shi sai kuma mahaifina.''

Asalin hoton, Reuters
Bayan da ya daina zuwa makaranta, Diop yana da shekara 12 lokacin da ya yanke shawarar barin koyon sana'ar dinkin kana ya fara sana'ar tseren sukuwar dawaki.
Kamar yadda mahaifinsa ya bayyana, ya yi tafiyar mil goma don ya isa wuri mafi kusa da ake yin rijistar atisayen sukuwar dawaki.

Asalin hoton, Reuters
Diop na zaune a gida tare sauran 'yan uwansa 12 a Niaga.
Nasarar da ya samu ta lashe kyautar kusan $600 kan ko wace gasar tseren ta ba shi damar saka sabon rufin kwano a gidansu.

Asalin hoton, Reuters
Adama Bao, wanda iyalansa suka shafe shekaru suna kiwon dawakai, shi ya koya wa Diop da sauran masu gasar sukuwar dawakan, a Niaga.
"[Diop] na da basira," in ji Bao.
"Zai iya shiga gasar har ya zuwa shekaru 50, saboda nauyi da kuma yanayin girman jikinsa.

Asalin hoton, Reuters
Sanye da kayan wasa masu launin rawaya da shudi, ba da dadewa ba Diop ya gwada basirarsa a bainar jama'a lokacin gasar tseren dawaki a Thiès, birni na uku mafi girma a kasar Senegal.

Asalin hoton, Reuters


Asalin hoton, Reuters
Ya yi nasarar zama zakara a uku daga cikin gasar tsere biyar da ya yi a wannan ranar, inda ya tafi gida da kyautar kusan $1,000.

Asalin hoton, Reuters
"Lokacin da na fara sukuwar, na rika jin wata damuwa, a cewarsa.
"Amma bayan zuwa dan wani lokaci, komai sai ya wuce.
"A lokacin gasar tseren, tunanin samun galaba kawai na rika yi."

Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka.











