Prince Philip: An kwantar da mijin Sarauniyar Ingila a asibiti

Prince Philip
An wallafa

An kwantar da mijin Sarauniyar Ingila Duke na Edinburgh a asibiti a ranar Talata da yamma "don a sa ido a kan lafiytarsa" bayan da ya nuna alamun rashin jin daɗin jikinsa, kamar yadda Fadar Buckingham ta ce.

Sanarwar masarautar ta ce an kai Yarima Philip mai shekara 99, Asibitin King Edward VII da ke Landan.

Wata majiya daga masarautar ta shaida wa BBC cewa an kai mijin sauarniyar asibitin ne da mota, inda aka kwantar da shi don sa ido a kan lafiyarsa kamar yadda likitansa ya bayar da shawara.

Ana sa ran zai ci gaba da kasancewa a asibitin tsawon ƴan kwanaki don ya samu hutu a kuma kula da shi.

Majiyar ta ce Yarima Philip ba shi da lafiya tswon kwanaki kaɗan, amma rashin lafiyar ba ta da alaƙa da cutar korona.

An kira wani likita sannan aka kai shi asibiti, sai dai majiyar ta ce rashin lafiyar ba ta yi tsanani ba, don haka ba a sashen gaggawa aka kwantar da shi ba.

A halin da ake ciki sarauniyar na fadarta da ke Windsor.

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan hakan.