Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barry Burgess: Tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC ya rasu
Muna alhinin sanar da ku rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC, Mista Barry Burgess.
Barry ya rasu a ranar Asabar din da ta wuce a gidansa da ke birnin Birmingham a Birtaniya yana da shekara 72 a duniya.
Maragayin ya rasu ne ba tare da ya yi jinya ba.
Ya soma aiki da BBC a shekarar 1974 a matsayin mai hada shiri a Sashen Hausa sannan ya bar BBC a matsayin shugaban sashen a shekarar 1999.
Bayan ya bar BBC, Barry Burgess ya koma koyar da harshen Hausa a tsangayar Nazarin Afrika da Gabashin Duniya da ke Jami'ar London.
An haifi Barry Burgess ne a ranar 8 ga watan Oktoban 1948.
Latsa alamar lasifika a hoton da ke ƙasa domin sauraren hirar da Is'haq Khalid ya yi da Mista Barry Burgess a 2017 lokacin bikin cikar BBC Hausa shekara 60 da kafuwa: