Muguntar da ƙungiyar IS ke yi wa mutane a Syria ta dawo

    • Marubuci, Daga Mike Thomson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Kungiyar IS ta kaddamar da hare-hare sama da 100 a arewa maso gabashin Syria a watan da ya gabata kawai kuma tana ci gaba da firgita garuruwa da ƙauyuka da dama daddare.

Tashin hankalin ya fi yawa a lardin hamada na Deir al-Zour.

Mai binciken nan na Syria Ali (sunansa na ainihi, tare da wata ƙungiya mai zaman kanta da yake yi wa aiki, mun ɓoye sunata saboda tsaronsa) suna tattara bayanai kan hare-hare.

Ya ce tashin hankalin ya dauki sabon salo.

"Sare kawunan mutane da sa abubuwan fashewa da kunar bakin wake a kan babura da kisan gilla da garkuwa da mutane - kuma duka wannan na faruwa ne a dan karamin yanki a gabashin birnin Deir al-Zour."

A daya daga cikin hare-haren baya-bayan nan, mutum 40 aka kashe a lokacin da wani mayakin IS ya kai hari kan wata motar bas.

Ali ya ce fararen hula sun fi shiga hatsari ne bayan almuru, lokacin da mayakan IS ke shiga yankin da ya zama mafi rashin tsaro.

"Idan dare ya yi suna cikin fargabar abin da zai zo masu daga mayakan IS. A baya su kan je ga hukumomi don neman tsaro amma ba a kai masu dauki.

"Ko yaushe sai su ce masu ba su da isassun makaman yaƙi, don haka sai su bar wurin. Bayan faɗuwar rana duka sojojin da ke da alaka da rundunar Syrian Democratic Forces sai su bar gari."

Amira (ba sunanta na ainihi ba) na da 'yan uwa a SDF, wata runduna da Kurdawa ke jagoranta, wadda kuma ke jagorantar yaki da IS a yankin tare da goyon bayan kawancen da Amurka ke jagoranta, inda ake korarta daga yankunan da masu ikirarin jihadin suka mamaye.

Amira ta ce birninta a yanzu ya zama abin tsoro idan dare ya yi.

"A yankin da nake zaune idan dare ya yi kusan ana iya cewa mayakan IS ne ke iko da shi. Suna yawo, suna kai hari gidaje tare da yi wa mutane barazana. Abin da ban tsoro... saboda su SDF ba su da wani iko da birnin idan dare ya yi... ko da rana ma. Babu ranar da ba za a kashe mutum daya ko biyu ba."

Kisa ba gargadi

Amira ta ce duk wani da ake tunanin yana da alaka da gwamnatin Syria ko SDF na cikin hadari. Sau da yawa mayakan IS na sa ma'aikatan gwamnati su ajiye aikinsu ko su fuskanci tashin hankali.

Wadanda masu ikirarin jihadin ke ganin sun da alaka da SDF kuwa kashe su kawai suke yi ba tare da gargadi ba.

Masu shaguna da sauran sana'o'i na shiga hadari, a kan aika masu sakonnin barazana ta waya ko a kira su a waya. Ana ba su umarnin biyan kudi masu yawa, wani lokaci yawan kudin kan kai $5,000 kuma idan ba su biya ba a kashe ko a yi garkuwa da wani daga iyalansu.

Wasu masu aikata laifuka da ke yankin sun samu wannan damar ta hanyar badda kama su nuna kamar su 'yan IS ne su rika tsoratar da mutane suna neman a ba su kudi.

Amira ta ce saboda jami'an tsaron kasar sun kasa shawo kan matsalar, ta kai ta kawo wasu mutanen ma 'yan tada kayar bayan suke kira su kawo masu dauki.

"Kwanan nan wasu mutum uku su ka yi ta wa wasu barazana, suna cewa su 'yan IS ne. Amma maimakon mutane su ba su kudi sai suka tambayi ainihin 'yan IS din idan da gaske mutanen nan 'yan kungiyarsu ne. IS suka ce ba 'yan kungiyarsu ba ne kuma suka kashe su duka ukun."

A lokacin da take kan ganiyarta, IS ta kafa daularta a Syria da Iraki, kuma girman wurin da ta ƙwace ya kai girman Burtaniya. Amma bayan fuskantar koma baya, masu ikirarin jihadin sun rasa yankinsu na karshe a watan Maris din 2019.

A lokacin, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa an murƙushe kungiyar "dari bisa dari", amma wannan ikirarin nasa na da alamar tambaya.

Bata, IS ta yi ikirarin kai hare-hare 600 a Syria da unguwannai sama da 1,400 a Iraki.

Akwai mayakan IS kusan 10,000 a Syria da Iraki, a cewar kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, kuma sakatarenta kan harkokin yaki da ta'addanci Vladimir Voronkov ya ce yana fargabar kungiyar na kara zama barazana.

"Bayan dakushe su a Iraki da Syria a 2019, IS ta fara gyagijewa tana sake yin shiri, kuma ta ci gaba da samun karfi," ya shaida wa BBC.

Wasu na fargabar cewa yanzu da gaba daya hankalin duniya ya karkata kan annobar korona, lamarin na kara lalacewa.

Cikin masu irin wannan tunanin har da Amira. Ta ce idan ba a kara kaimi wajen yaki da su ba, mutanen kasar da dama na da tunanin cewa idan ba za a iya yakarsu ba, to mu ma bari mu shiga cikinsu.

"Idan lamarin ya ci gaba yadda ya ke, ina ganin mutane za su koma suna goya wa IS baya a yankin. Saboda lokacin da IS ke da iko, lallai da ban tsoro kuma suna kashe mutane, amma mu kan samu tsaro ta wani fannin, ba kamar yanzu ba."