Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An haramta amfani da kuɗin intanet, an yi wa Boko Haram luguden wuta
Abubuwa da dama ne suka faru a Najeriya a makon da ya gabata, ciki har da haramta amfani da kuɗin intanet da tsawaita wa'adin aikin Sufeto Janar na 'yan Sanda da yi wa 'yan Boko Haram luguden wuta.
Mun duba muhimmai daga cikinsu.
Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta amfani da kuɗin intanet
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan ƙasar da su rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kuɗin intanet na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban 'yan ƙasar daɗi ba.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a ga bankunan hada-hadar kuɗi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kuɗi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kuɗi.
"Ƙari a kan umarnin da aka bayar tun a baya, bankin (CBN) yana tunatar da ma'aikatun da ke mu'amala da kuɗaɗen intanet ko kuma dillalansu cewa haramun ne," a cewar sanarwar.
A shekarar 2017, CBN ya ce kuɗaɗen intanet irin su bitcoin da litecoin da sauransu ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta'addanci da kuma halasta kuɗin haramun, ganin cewa ba a iya bin sawunsu.
"Saboda haka, an umarci dukkanin NBFIs da NBFIs da OFIs da su tantance mutanen da ke amfani da irin waɗannan kuɗaɗe sannan su rufe asusun ajiyarsu," a cewar umarnin.
Buhari ya tsaiwata wa'adin Sifeton Janar na 'yan sandan Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin Babban Sufeton 'yan Sandan ƙasar, Mohammed Adamu.
Buhari ya bayyana haka ne a sakon da masu taimaka masa kan harkokin watsa labarai suka fitar da yammacin Alhamis.
Ya tsawaita wa'adin Babban Sifeton 'yan sandan ne da wata uku.
Sakon ya ambato Ministan kula da harkokin 'yan sanda, Maigari Dingyadi yana bayyana hakan a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
A ranar Litinin 1 ga watan Fabarairu ne Mr Adamu ya kamata ya yi ritaya daga aiki bayan da ya shafe shekara 35 yana aiki, kamar yadda tsarin aikin dan sanda ya tanada.
Gwamnan Kano ya haramta wa Sheikh Abduljabbar Kabara wa'azi tare da rufe masallacinsa
Majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa fitaccen malamin addinin Islama na jihar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar nan take.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammadu Garba ne ya tabbatar wa da BBC ranar Laraba.
Ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar na ranar Laraba bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa malamin na yin kalaman da ka iya haifar da fitina a jihar.
''Gwamnati ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro, dalilin da ya sa jami'an tsaro suka sanya kwamiti na musamman don duba irin waɗannan kamalamai da malamin ke yi'' a cewarsa.
Ya ce sakamakon tattaunawa a kan wannan batu da majalisar zartarwar jihar Kanon ta yi ne yasa ta amince da cewa, ba shakka kalaman nasa na iya haifar da tarzoma, don haka ta bada umarnin hana shi yin wa'azi a ko ina a faɗin jihar.
Sojojin Najeriya sun yi wa Boko Haram luguden wuta a Dajin Timbuktu
Dakarun sojin Najeriya ƙarƙashin Shirin Lafiya Dole mai yaƙi da Boko Haram sun yi luguden wuta a Timbuktu, wani ɓangare mai sarƙaƙiya a dajin Sambisa da yankunan kusa da Tafkin Chadi.
A ranar Laraba ne rahotanni suka ruwaito cewa sojoji sun kwashe tsawon mako guda suna ɗauki-ba-daɗin fatattakar 'yan ta-da-ƙayar-baya a yankin, abin da kuma ya yi sanadin mutuwar gomman 'yan Boko Haram.
Bayanai sun ce Dajin Timbuktu, wanda ya ratsa tsakanin jihohin Borno da Yobe, ya yi ƙaurin suna don kuwa a tsawon shekara huɗu da suka gabata, sojoji sun gaza shigarsa ta ƙasa.
Bayanai sun ce aikin fatattakar wanda ke ci gaba da gudana ya yi sanadin 'yantar da Buk da Talala da Gorgi waɗanda dukansu tungar 'yan Boko Haram ne da ke da ƙarfi.
Amurka ta amince Ngozi Okonjo-Iweala ta jagoranci WTO
Gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta kawo ƙarshen takaddamar da ta hana naɗa mace ta farko da za ta jagoranci Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) bayan da ta bayyana goyon bayanta ga tsohuwar ministar kuɗin Najeriya.
Ngozi Okonjo-Iweala ce ke kan gaba wajen zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar cinikayyar ta duniya kafin gwamnatin Mista Trump ta ce tana goyon bayan wata matar ta daban, Yoo Myung-hee ta Koriya ta Kudu.
A halin da ake ciki, Ms Yoo ta janye daga takarar shugabancin ƙungiyar.
Idan aka tabbatar ma ta muƙamain, Dr Okonjo-Iweala za ta kasance mace ta farko, kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa gwamnatin Amurka bisa goyon bayan da ta nuna wa tsohuwar ministar kuɗin, yana mai cewa "'yan Najeriya da 'yan Afirka baki ɗaya na murna da wannan sabon mataki".
An kori makiyaya 37 da shanu 5,000 daga Jihar Ondo
Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar tsaro ta Amotekun ta kori makiyaya 37 da shanunsu kusan 5,000 daga dajin Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Wannan ya biyo bayan umarnin da Gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya bayar ne ga Fulani makiyaya da ko dai su yi rajista da gwamnati ko kuma su bar jihar, bayan an zarge su da zama a dazukan ba bisa ƙa'ida ba.
Shugaban ƙungiyar ta Amotekun a Ondo, Chief Adetunji Adeleye wanda ya bayyana hakan, ya ce wasu daga cikin makiyayan sun zaɓi su bar jihar ne cikin ruwan sanyi saboda dokokin da aka saka musu sun yi tsauri.
Ya ce an kori mutanen ne daga garuruwan Ala da Oda da kuma dajin Ofosu.
A daina kai wa Fulani hare-hare a kudu - Gwamnonin Arewa
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi kira da a daina kai wa ƙabilar Fulani da ba su ji ba su gani ba a yankin kudu maso gabas da kudu maso yamma da kuma kudu maso kudancin ƙasar hare-hare.
Gwamnonin sun bayyana cewa ba daidai ba ne a riƙa kai hari ga Fulanin da ba su ji ba su gani ba.
Kazalika sun buƙaci a riƙa miƙa wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka hannun hukuma a maimakon daukar doka a hannu.
To sai dai takwarorinsu na Kudu maso Yammacin ƙasar sun yi martani, inda suka buƙaci shugabanni a yankin arewa da su ja kunnen yan ƙabilar Fulani da ke kai hare-hare a can.
An ƙara wa'adin haɗa lambar NIN da layukan waya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tsawaita wa'adin haɗa lambar ɗan ƙasa ta NIN da layukan salula wanda ake gudanarwa yanzu haka da kusan wata biyu.
Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan yayin wani taron ministoci kan haɗa lambar NIN da lambar waya a jiya Litinin.
Rahoton ƙarin wa'adin na cikin wata sanarwa ce da shugaban sashen sadarwa na hukumar samar da katin ɗan ƙasa ta NIMC ya fitar a yau Talata, inda Pantami ya ce za a ci gaba da aikin har zuwa 6 ga watan Afrilun 2021.
Ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa 'yan Najeriya da kuma 'yan ƙasashen waje damar haɗa lambobin nasu da layukan wayarsu.
Sanarwar ta ce ya zuwa yanzu kamfanonin sadarwa sun karɓi lambar NIN ta mutum miliyan 56.18.
"A mataki na tsakatsaki, kowace lambar NIN na ƙunshe da lambobin waya uku zuwa huɗu, kuma hakan na nufin wannan adadi shi ne na mafi yawan layukan wayar da ke aiki a yanzu," in ji sanarwar.
"Adadin ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da miliyan 47.8 da aka samu a Janairun 2021."
An yanke wa mutum 100 hukunci a Abuja kan ƙin sanya takunkumi
Wata kotun tafi da gidanka a Najeriya ta yankewa mutum fiye da 100 waɗanda suka karya ka'idojin kariya daga cutar korona hukuncin biyan tara a Abuja.
Kotun ta yankewa mutanen ne hukunci bayan ta same su da laifin ƙin sanya takunkumi a cikin jama'a.
Facebook ya rufe shafin shugaban ƙungiyar IPOB Nnamdi Kanu
Facebook ya cire shafin shugaban ƴan awaren nan na IPOB a Najeriya, Nnamdi Kanu, bayan wani bidiyo da ya fitar ranar Talata inda yake zargin makiyaya da lalata gonaki.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya a sassa da dama na ƙasar.
Mista Kanu ya wallafa bidiyon wasu mutane da ake zargin ƴan kungiyar Eastern Security Network ne - wata kungiyar mayaƙan sa kai a kudu maso gabashin Najeriya - suna karkashe shanu a unguwannin makiyaya.
Buhari ya mayar wa Nnamdi Kanu martani
'Sojoji sun kai samame gidan jagoran Biafra'
Maryam ta iya yaren Igbo sosai duk da cewa bafulatana ce
Mai magana da yawun Facebook ya shaida wa BBC cewa burin kamfanin shi ne "bai wa mutane damar yin magana" amma kuma yana so mutane su "san cewa suna cikin tsaro" a lokacin da suke kan shafin.
A wata sanarwa, Facebook ya ce cire shafin Nnamdi Kanu ya bi tsarin dokokinsa ne na wallafa sakonni masu dauke da kalaman ɓatanci.