Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Nijar: Jam'iyyn Nijar na wasa wuƙarsu gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa
Ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu ce za ta zamo ranar raba gardama tsakanin 'yan takara 2 wadanda suka taka rawar gani da yawan kuri'u a zaben shugaban kasa zagayen farko a jamhuriyyar Nijar.
'Yan takara na daya da na biyu su ne za su sake fafatawa tare da hadin gwiwar sauran jam'iyyun da suka kulla kawance da su domin su kawo masu goyon baya da gudummuwar kuri'u daga magaya bayansu.
A wannan karo zaben zai kasance tsakanin Mahamane Ousmane na jam'iyar RDR-Canji da kuma Mohamed Bazoum na jam'iyar PNDS Tarayya wacce yanzu haka ita ce ke kan mulkin kasar.
Wani abu game da 'yan takarar guda biyu, shi ne dukkansu sun fito ne daga jihar daya - Damagaram wato Zinder da ke yankin gabas maso kudancin kasar, kuma yankin da ke iyaka da kasar tarrayar Najeriya.
A yanzu haka dai dan takara Mohamed Bazoum ya samu goyon bayan jam'iyu biyu da suka zo na uku da na hudu wajen yawan kuri'u a zagayen farko na zaben.
Sun hadar da jam'iyar MNSD -Nasra da Seiny Oumarou ke jagorenta da kuma MPR Jamhuriya da Albade Abouba ke jagorenta.
A dai wa'adin baya na jam'iyyar ta PNDS Tarayya karkashin jagorencin Shugaba Mahamadou Issoufou, wadannan jam'iyyu na tare da jam'iyyar mai mulki bayan sun ƙulla ƙawance.
Abun tuni a nan shi ne, a tarihin zaben dimokaraɗiyya a kasar Nijar, babu wata jam'iyar siyasa guda tillo da za ta iya kafa gwamnati ita kadai, dole ne sai an samu kawancen sauren jam'iyyun siyasa tare da ita.
Haka zalika ko da yaushe sai an je zagaye na biyu sabili da babu jam'iyyar da dan takarar ta zai iya samun kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada lokacin zaben farko domin ya wuce nan take a zagaye na farko.
Duk da cewa daga cikin jam'iyyun da suka ƙulla ƙawance da jam'iyya mai mulki domin ci gaba da jagorancin kasar idan suka yi nasara to wasu 'yan kasa ba su ji dadin wannan kawance ba da jam'iyyun suka ƙulla da jam'iyyar mai mulki.
Wasu ma sun yi barazanar ƙin kaɗa ƙuri'unsu ga jam'iyyar da jam'iyyarsu ta ainahi ta ƙulla ƙawance da ita.
Yanzu dai ta na kasa ta na dabo, tsakanin jam'iyyun biyu masu takarar kujerar shugaban kasa zagaye na biyu kuma na ƙarshe.