Ana fargabar ɓarkewar yaƙin basasa a Afghanistan

An wallafa

Wanni babban jam'in diflomasiya daga ƙungiyar Tarayyar Turai da ke ziyara a Afghanistan ya sanar da cewa ''akwai haɗari mai girman gaske game da yiwuwar ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar ganin yadda tashe -tashen hankula ke ci gaba da ƙazanta.

Kwamishinan kiyaye zaman lafiya da yaƙi da tashin hankali na ƙungiyar Janez Lenarcic, ya ce da akwai gagarumar alama da ke nuna cewa, babu wata nasara kan hanyoyin da ake bi wajen samar da zaman lafiya da aka soma a watan Satumbar da ya gabata, hanyoyin da tuni ake gani suna da matsala.

Jam'in ya buƙaci yin dukkan ƙoƙarin da ya dace wajen ganin cewa tattaunawa tsakanin gwamnati da wakilan 'yan kungiyar Taliban ba ta sha ruwa ba.

Ya kuma yi kira ga 'yan Taliban da ke kai hare-hare, da su kara yin kokari fiye da wanda suka yi a baya, wajen ganin wannan tattaunawa ta gudana.

Mista Lenarcic ya furta cewa, kusan rabin al'ummar kasar Afghanistan na ƙishirwar ganin an kawo karshen wannan tashin hankali da ke gudana, wanda kuma a halin da ake ciki ke haddasa mumunan yanayi ta bangaren aikin jin kai.

Jam'in ya kuma furta ƙarara cewa, gwamnatin Afghanistan sai ta yi da gaske wajen kawar da cin hanci da rashawa a cikin kasar.

Tun 1996 kungiyar ta Taliban take iko da mafi yawancin kasar Afghanistan har zuwa lokacin da sojin hadaka da Amurka ta jagoranta suka fatattake su a 2001.

Hakan ne ya sanya gwamnati take ta neman 'yan kungiyar da su shiga a dama da su a gwamnati amma sun sha yin watsi da hakan.

Ana kuma tunanin kasancewar sojojin kasashen waje a kasar ne ya sanya 'yan kungiyar kara bujirewa.