Manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a makon jiya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Mafi yawan abubuwan da suka fi daukar hankali a labaran Najeriya sun shafi matsalolin tsaro ne, don haka ko makon da ya gabata cike yake da kalubalen tsaro a wasu daga cikin sassan kasar.

Abubuwa da dama sun faru sai dai ga wasu daga cikin muhimmansu a takaice:

An bai wa makiyaya umarnin fitas daga dazukan jihar Ondo

An shiga makon ne da ce-ce-kuce sakamakon wani wa'adin mako daya da gwamnan jihar Ondo ya bai wa makiyaya su fita daga dazukan jihar.

Gwamana Rotimi Akeredolu, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya dora alhakin satar mutane da wasu laifuka kan makiyayan.

Fulani makiyaya a jihar Ondo sun ce sanarwar ta zo masu da mamaki.

Sarkin Fulani na jihar Alhaji Ali Dogo ya ce sanarwar ta zo masu da mamaki ne saboda sun cimma matsaya da gwamnan jihar a baya.

"Ban ji daɗi ba saboda mu ƙungiyar Fulani makiyaya mun je har gaban gwamna aka ce mu haɗa kai da gwamnan zai ba mu kayan aiki mu yi maganin duk wani mugu," in ji shi.

Ita ma gwamnatin tarayyar kasar ta ce ba ta amince da wannan matsaya ba ta gwamnan jihar Ondo domin kuwa hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar da ya bai wa kowanne dan kasar damar zama a kowanne sashe na kasar.

Yadda 'yan bindiga 'suka kashe mutum 37 a wani kauyen jihar Zamfara'

A makon na jiya ne kuma daruruwan mazauna wasu kauyuka suka tsere daga muhallansu zuwa garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara ta arewa masu yammacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne sakamakon hare-haren 'yan fashi na baya-bayan nan da suka tilasta musu yin gudun hijira.

Kauyuka sama da biyar ne wadannan hare-hare suka shafa wadanda suka hada da Dutsen Gari da Telli da Tsakuwar dan Abara da Fara Girke.

Maharan sun kona gidaje da dukiyar da har yanzu ba a san adadinta ba.

Wani mazaunin kauyen Dutsen Gari ya shaida wa BBC cewa an kashe mutum 37 a kauyen nasu a ranar Litinin, sannan maharan suka afka wa sauran kauyukan ranar Talata.

Harin da aka kai wa Fulani a Jihar Oyo

Wasu Fulani makiyaya da ke zaune a jihar Oyo ta kudu maso yammacin Najeriya sun yi zargin cewa wasu 'yan banga da ke ikirarin kare kabilar Yarbawa sun kai musu hari ranar Juma'a.

Harin ya yi sanadin mutuwar matar Malam Aliyu dan sarkin Fulanin jihar ta Oyo, a cewarsa.

Wannan hari na zuwa ne a yayin da wa'adin da jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya su bar dazukan jihar ko kuma a tliasta musu yin hakan ya zo karshe.

Gwamnatin jihar Oyo ta ce ba ta bayar da umarnin a kai wa Fulani makiyaya hari ba, kuma ba ta goyon bayan hakan.

Ƙalubalantar da Bafarawa ya yi wa gwamnatin Najeriya kan lamarin tsaro

Tsohon gwamnan Sokoto, Dr Dalhatu Attahiru Bafarawa wanda kuma jigo ne a siyasar arewacin Nijeriya ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fifita yaƙi da 'yan fashin daji kamar yadda take yi wa annobar korona.

Dr Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi gwamnati ta kafa kwamiti na musamman da zai sa-ido kan kuɗaɗen da ake kashewa kan harkar tsaro, don yi wa 'yan ƙasa bayani dalla-dalla ta yadda za a tabbatar da tsare gaskiya da kawar da duk wani zargi.

Tsohon gwamnan jihar Sokoton ya shaida wa BBC cewa yaƙin da gwamnati ke yi da ta`addanci ba zai yi nasara ba, sai an samu haɗin kan `yan ƙasa gaba ɗaya.

A cewarsa, "kamata ya yi a sa mutane waɗanda abin ya shafa, za ka ga wani mutum yana nan bai iya rubutawa bai iya karantawa amma idan aka nemi shawara ta ƙauyensu, zai ba da shawarar da za ta fi ta manjo ma."

Mayar da 'yan Najeriya gida wandanda suka maƙale a Saudiyya

Wani bidiyo da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna wasu da ake tunanin ƴan Najeriya ne da suka maƙale a Saudiyya.

Babu tabbas kan wanda ya naɗi bidiyon saboda bai nuna fuskarsa ba amma an jiyo muryarsa yana kira ga gwamnatin Najeriya ta kawo masu ɗauki.

"Ina miƙa gaisuwata da godiyata a gareku yan siyasar ƙasata da aka zaɓa. Burin wannan bidiyon shi ne don in nuna maku halin da mu ƴan Najeriya muke ciki a nan Saudiyya tsawon wata shidda," a cewar mutumin wanda ya yi magana da harshen turanci.

Bidiyon bai daɗe da fita ba sai shugabar Hukumar da ke kula da harkokin ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter inda ta ce mutanen da ke cikin bidiyon ƴan Najeriya ne da suka shiga Saudiyya ba a bisa ƙa'ida ba.

ta kuma ce "Za a dawo da ƴan Najeriya da suka shiga Saudiyya ba a bisa ƙa'ida ba ranar 28 da 29 na wannan watan na Janairu idan shirin da muke yi ya tafi yadda muke so. Dama an samu tsaiko ne wajen ɗebo su saboda annobar korona," kamar yadda ta wallafa.

Kalaman Jega kan sauya fasalin Najeriya

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce samun shugaba mai adalci shi ne babban abin da ya kamata 'yan kasar su sanya a gaba maimakon ce-ce-ku-cen da ake yi na sake fasalin kasar.

Farfesa Jega ya bayyana haka ne yayin da al`umomin bangarorin kasar ke neman a sake fasalin mulkin kasar ta hanyar komawa ga tsarin lardi-lardi ko shiyya-shiyya, wasu kuma na ganin cewa kamata ya yi a inganta tsarin da ake kai na jihohi 36 da kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar.

Tsohon shugaban INEC kuma masanin siyasa, Farfesa Jega, ya shaida wa BBC Hausa cewa ya kamata a inganta tsarin da ake kai na jihohi 36 da Abuja.