Zaɓaɓɓun hotuna masu ƙayatarwa daga faɗin Afrika da kewaye:
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Litinin dan wasan gaba na Arsenal kuma dan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ya yi murnan cin kwallo ta farko a wasan da suka buge da Newcastle United.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Talata Kirisotoci na gargajiya a Habasha masu ibada a Gondar suna nunƙaya a yayin bikin Timkat,
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ... Manyan limaman Kiristocin Habasha sun jeru a babban birnin kasar Addis Ababa yayin bikin...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ... da ake murnar wankan tsarkin Yesu Kiristi a tafkin Jordan...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ... Mata mabiya addinin Kiristanci sanye da fararen kaya yayin bikin.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ranar Lahadi a babban birnin Masar Alkahira an yi holen wata daɗiyyar gawa ta Masar yayin da ake shelanta gano gagarumar ajiyar a ƙarƙashin ƙasa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Juma'a Mabiya ɗariƙun Sufaye a Sudan sun taru a wajen hubbaren Hamad al-Nile a Omdurman.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Litinin an bude makarantu a Ghana bayan shafe wata goma a rufe a yunƙurin rage yaɗuwar cutar korona.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar ne kuma ma'aikatan lafiya ke shirin kama aiki a babban asibitin Kamuzu a Lilongwe, Malawi.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Jami'an lafiya na sanya wani mutum da ya nuna alamun cutar korona cikin wajen da za a killace shi a kusa da birnin Pretoriya a Afirka ta Kudu ranar Juma'a
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Litinin shugaban Kotun Tsarin Mulki ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Daniele Darlan ya tabbatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a watan Disamba, wanda aka sake zaɓar Faustin-Archange Touadéra a matsayin shugaban ƙasa...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ... sakamako haka, magoya bayansa suka nufi babban ofishin jam'iyyarsa, the Movement of United Hearts.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar Asabar magoya bayan Yoweri Museveni sun yi murna bayan an sake zaɓensa a matsayin shugaban Uganda...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...babban abokin hamayyyarsa Bobi Wine,da aka ɗauki hotonsa a ranar Juma'a ya ce zaɓen zamba ne.