Fashewar Iraƙi: IS ta ce ita ce ta kai hare-haren ƙunar bakin waken Baghdad

An wallafa

Kungiyar Islamic Group (IS) ta ce ita ce ta kai hare-haren bam biyu na ƙunar baƙin wake a Baghdad babban birnin kasar Iraƙi a ranar Alhami wanda ya kashe a kalla mutum 32 kuma ya raunata fiye da mutum 100.

Wadanda aka kai wa harin dai mabiya mazhabar Shi'a ne, kamar yadda wata sanarwar da kafar yada labarai mllakin 'yan Sunni na kasar ta sanar.

Wannan ne hari mafi girma da muni a Baghdad cikin shekara uku.

Maharan sun tayar da bama-baman yayin da suke cikin tarin jama'a da ke hada-hadar saye da sayarwa a wata kasuwar kayan gwamnjo a dandalin Tayaran.

Wannan sakon daukan alhakin da kungiyar masu tayar da kayar baya ta yi, wanda ta fitar da shi ta wasu shafukanta na manhajar sadarwa ta Telegram ya zo ne sa'o'i bayan kai harie-haren.

Hare-haren ƙunar baƙin wake sun kasance abubuwan da ba a cika kin karo da su ba a Baghdad tun bayan da aka fatattaki IS a yankin a karshen shekarar 2017.

Amma duk da kayen da IS ta sha, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a watan Agustan bara na cewa kimanin mayaka 10,000 na kungiyar na nan suna yaki a Iraƙi da Syria.