Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Messi, Haaland, Alli, Alaba, Tomori, En-Nesyri, Lingard da Buendia
Daraktan wasannin Paris St-Germain Leonardo ya dage cewa har yanzu kungiyarsa tana son sayen dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, wanda kwangilarsa a Barcelona za ta kare a bazarar nan. (Sport)
Chelsea ta shirya kafa tarihi na sayen 'yan kwallon kafa inda za ta sayi dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, mai shekara 20, a bazarar nan, duk da yake sai a shekarar 2022 za a biya kudin darajar dan wasan na Norway wato €75m (£66.6m). (The Athletic - subscription required)
PSG tana sa ran yanke hukunci a wannan makon game da burinsu na daukar dan wasan Tottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 24. (Mirror)
Wani babban jami'i a AC Milan Paolo Maldini ya ce sun kusa kammala karbo aron dan wasan Chelsea dan kasar Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 23. (Sky Sports)
Real Madrid ta amince ta sayi dan wasan Bayern Munich dan kasar Austria David Alaba, mai shekara 28, a bazara. (Marca)
Dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, wanda ake hasashen zai tafi Tottenham, West Ham, Marseille ko kuma Inter, yana son barin kungiyar amma kocinta Ole Gunnar Solskjaer ba ya so ya sake shi a wannan watan. (ESPN)
Ralph Hasenhuttl ya dage cewa "lamura za su ci gaba kamar yadda aka saba" idan dan wasan Ingila Danny Ings ya bar Southampton domin tafiya wata babbar kungiyar a bazara saboda kungiyarsu ba za ta iya biyan bukatun da dan wasan mai shekara 28 ya sanya a kwangilarsa ba. (Mirror)
Akwai bukatar Arsenal ba bai wa Norwich tsakanin £40m zuwa £50m idan tana so ta amince ta sayar mata da dan wasan Argentina Emi Buendia, mai shekara 24. (Sky Sports)
Dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 28, wanda ake hasashen zai tafi Real Madrid, ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da murza leda a Anfield har bayan karewar kwangilarsa a 2023, amma ya ce makomarsa "tana hannun kungiyar". (90 Min)
Dan wasan Galatasaray da Senegal Mbaye Diagne, mai shekara 29, yana cikin jerin 'yan kwallon da West Brom take son dauka a wannan watan. (Express & Star)
West Ham ta nemi daukar dan wasan Sevilla dan kasar Morocco Youssef En-Nesyri, mai shekara 23. (The Athletic - subscription required)
AC Milan da West Ham sun nemi daukar dan wasanBarcelona dan kasar Sifaniya Junior Firpo, mai shekara 24, wanda ba a saka shi a tamaula. (ESPN)
Zai yi matukar wahala a tantance makomar dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a watan nan amma watakila a samu matsaya a bazara mai zuwa. (Sky Sports)