Covid-19: Hanyoyin da za ku kare 'ya'yanku daga kamuwa da cutar korona yayin da aka bude makarantu

An wallafa

Galibin jihohin Najeriya sun bi sahun wasu kasashen duniya wajen sake bude makarantu a ranar Litinin 18 ga watan Janairu a yayin da kasar ke ci gaba da fama da annobar korona.

Akasarin gwamnatocin jihohin kasar sun sake bude makarantun firamare da sakandare da ma na gaba da sakandare.

Sai dai jihohi irin su Kaduna da Edo ba su bude makarantun ba suna masu cewa yin hakan zai kara yada cutar ta korona musamman ganin cewa a yanzu ne take kara kama mutane. Sun ce sai sun kammala sanya matakan kariya a makarantun kafin a sake bude su.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC, ta fitar sun nuna cewa karin mutum 1,444 sun kamu da cutar ta korona a kasar ranar Lahadi.

A yayin da ake sake bude makarantun, hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, UNICEF, ta fitar da wasu hanyoyi da za su taimaka wa iyaye da makarantu wajen kare 'ya'yansu da ma'aikata daga kamuwa daga cutar korona.

UNICEF ta bayar da shawara ga hukumomi su bambanta ranakun sake bude makarantu da kuma rufe su idan an tashi.

Sauran shawarwarin sun hada da bambanta lokutan fita cin abinci tsakanin azuzuwa, da lokutan tafiya hutun tara.

Kazalika UNICEF ta bukaci makarantu su samar da bokitai da sabulai da man sanitaiza da kuma sauran abubuwan tsafa yadda dalibai da malamai da sauran ma'aikata za su rika tsarkake hannayensu.

UNICEF ta bukaci nemi kowanne dalibi ya sanya takunkumi sannan a gwada zafin jikinsa kafin ya shiga makaranta.

Ɗana yana jin tsoron komawa makaranta. Yaya zan taimaka masa domin ya kwantar da hankalinsa?

Wasu magidanta sun shaida wa BBC cewa 'ya'yansu suna tsoron komawa makaranta a yayin da aka sake bude makarantu ranar Litinin saboda fargabar kamuwa da Covid-19.

Dalibai da dama musamman wadanda ke koyon karatu daga gida sun ce sun fi so su ci gaba da yin karatu daga gida saboda suna ganin zai yi wahala su tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna idan suka je makaranta.

Masana harkokin lafiya sun bukaci iyaye su shaida wa 'ya'yansu su yi biyayya ga dokokin kare kai daga kamuwa daga cutar korona idan suka je makaranta.

Sun ce idan dalibi ya sanya takunkumi, ya yi nesa-nesa da abokinsa, ya wanke hannunsa, ya kuma rufe bakinsa da gwiwar hannunsa yayin da zai yi atishawa, matakan za su takaita yaduwar cutar.

Yadda cutar ke yaduwa

Wani abu da ya kamata a tunawa dalibai shi ne yadda cutar korona take yaduwa.

Kamar yadda masana kiwon lafiya suka sha fada, cutar korona tana saurin yaduwa fiye da yadda ake zato, in ji wani kwararren likita Dr Nasir Sani Gwarzo.

A cewarsa: "Ana ganin idan mutum daya ya kamu, a cikin yini guda zai iya shafa wa mutum uku zuwa tara. Sannan a cikin kwana shida adadin zai iya ninkawa wajen hawa tara a cikin kankanin lokaci.''

Ya kara da cewa, "Misali idan mutum yana cikin taro, sai ya yi atishawa ko ya yi kaki ya tofar ko kuma ya face majina da hannunsa to zai iya shasshafa wa mutane a hannayensu."

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana karin matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar korona.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

An rikita kan dalibai

A yayin da wasu makarantu musamman jami'o'i suka dora kan jadawalin karatunsu, wasu sun soke kalandarsu inda za a soma sabuwar kalandar karatu maimakon dorawa daga inda aka tsaya gabanin rufe makarantun.

Jami'o'i irin su Jami'ar Bayero da ke Kano sun soke shekarar karatu ta 2019/2020, yayin da Ahmadu Bello da ke Zaria ta ce za ta karasa shekarar karatun ta 2019/2020.

Hakan zai sa a samu bambancin kammala shekarun karatu a jihohi daban-daban na Najeriya.