NECO 2020: Yadda za ku duba sakamakon jarrabawar a shafin intanet

NECO

Asalin hoton, NECO

An wallafa

Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya, National Examinations Council (NECO), ta fitar da sakamakon jarrabawar na sakandire ta shekarar 2020.

Shugaban hukumar, Godswill Obioma ne ya bayyana hakan ranar Laraba a hedikwatar NECO da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Dalibai 1,221,447 ne suka yi rijistar jarrabawar, cikinsu maza 665,830 yayin da mata 555,617.

A cewar Obioma, dalibai 1,102,041 cikin dalibai 1,209,992 da suka zana jarrabawar sun samu credit zuwa sama yayin da dalibai 894,101 suka samu credit zuwa sama a Turanci da Lissafi.

Shugaban hukumar ya ce an kama dalibai 33,470 da laifin satar amsa yayin da aka samu makarantu 12 da kama malaman da ke sa ido a kan dalibai 24 da hannu a satar amsa.

Ga yadda za ku duba sakamakon jarrabawar NECO a shafin intanet:

  • Za ku sayi token sannan ku duba sakamakon jarrabawar NECO idan kuka shiga shafinsu na intanet: www.neco.gov.ng
  • Ku duba shekarar da kuka yi rijistar jarrabawarku, misali 2020
  • Ku duba jarrabawar da kuka yi rijistar zanawa misali, SSCE INTERNAL (JUN/JUL)
  • Sai ku shigar da lambar Token da kuma lambar da kuka yi rijista a guraben da za a nuna muku
  • Daga karshe, ku latsa madannin check result domin ganin sakamakon jarrabawar NECO.

Idan kuka bi wadannan matakai, za ku ga sakamakon jarrabawarku ta NECO.