Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Diary Sow: Ɗalibar 'da ta fi hazaƙa' a Senegal ta ɓata a Faransa
An soma gudanar da bincike a Faransa bayan ɓatan wata ɗaliba 'yar ƙasar Senegal wacce take karatu a wata shahararriyar makaranta a Paris.
Diary Sow ba ta koma makarantar ba bayan hutun Kirsimeti, abin da ya janyo damuwa a Senegal da Faransa.
Ms Sow, wadda aka bayyana a matsayin "ɗaliba da ta fi hazaƙa a Senegal", ta lashe kyautuka da dama a ƙasar kuma ta wallafa littafi a shekarar da ta wuce.
Ba a ga ɗalibar mai shekara 20 ba tun ranar 4 ga watan Janairu.
Fitattun 'yan ƙasar Faransa da dama, cikinsu har da tauraron fina-finai Omar Sy, suna ta yekuwar nemanta a shafin Instagram da Twitter.
Ya wallafa wallafa hotunan yekuwar a Twitter:
Ms Sow ɗaliba ce 'yar aji biyu a makarantar Lycée Louis-Le-Grand ta birnin Paris, bayan ta samu tallafin karatu saboda basirarta.
"Ɗaliba ce da ke yin komai a kan lokaci, mai himma, kuma mun soma nemanta ne nan da nan. Babu wanda ya gan ta, ba mu gan ta a gidan da take zaune ba" wanda ke cikin jami'ar ta Paris, a cewar Henry Sarr, wani mamba na ƙungiyar ɗaliban Senegal waɗanda suke fafutukar nemanta, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"'Iyayenta da ƙawayenta da masu riƙonta da kuma ofishin jakadanci ba su samu labari a game da inda take ba," a cewar wani mamba na ƙungiyar 'yan asalin Senegal da ke Paris - Daouda Mbaye a hirarsa da AFP.