Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda aka yi wa wasu shugabannin duniya riga-kafin korona
An yi wa zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Joe Biden allurar rigakafin korona a ranar 21 ga watan Dismabar bara, inda wata malamar jinya ta yi masa allurar a wani asibiti a Newark da ke jihar Delaware ta ƙasar.
Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum shi ne mutum na farko da aka fara yi wa riga-kafin korona a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Sheikh Mohammed, wanda shi Firaiministan ƙasar, ya wallafa hotonsa a shafinsa na Twitter tun a ranar 3 ga watan Nuwamba. Haka kuma yana daga cikin shugabanni na farko da aka fara yi wa riga-kafin a duniya
Shi ma Yariman Saudiyya, Mohammed Bin Salman ba a bar shi a baya ba, inda tun a ranar 25 ga watan Disambar bara aka yi masa allurar
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kenan yayin da likitansa, Dakta Tzvi Berkovitz ke yi masa allurar riga-kafin korona a asibitin Sheba da ke birnin Ramat Gan a ranar 19 ga watan Disamban 2020.
Shugaban shi ne ɗan ƙasar na farko da aka fara yi wa allurar.
Ita ma Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosy, an yi mata allurar, inda Dakta Brian Monahan ya je har ofishinta da ke Capitol Hill a Washington DC ya yi mata riga-kafin a ranar 18 ga watan Disamban 2020.