Covid-19: Yadda cutar korona ta yi ajalin uwa a gaban ƴarta da suke jinya a asibiti ɗaya

Maria and Anabel in hospital

Asalin hoton, Anabel Sharma

An wallafa

Wata mata da mahaifiyarta ta mutu a gabanta sakamakon annobar korona ta gargaɗi mutane da su bi dokokin korona.

Mahaifiyar dai ta yi jinya ga gado ga gado da ɗiyarta a asibiti, inda har sai da cutar ta yi ƙamari ta sa aka saka musu na'urar taimaka wa numfashi dukkansu.

Maria Rico, mai shekara 76, ƴar asalin Leicestershire ce, ta cire na'urar taimaka mata wurin numfashinta, inda ta yi wa ƴaƴanta biyu magana ta ƙarshe - duk da cewa ta san hakan zai sa ta yi saurin mutuwa.

Anabel Sharma, ta bayyana lokacin a matsayin "mai karya zuciya" amma ta ce ta ji daɗi mahaifiyarta ba ita kaɗai ta mutu ba.

Hakan ya sa ta saki hotunan su na ƙarshe da suka ɗauka domin ta wayar da kan mutane kan cutar.

Ta'aziyya

Misis Sharma da ke ƙauyen Whitwick a Ingila, ta bayyana cewa mahaifiyarta ta mutu mintuna talatin bayan an cire mata na'urar taimaka mata wurin numfashi.

"Mahaifiyata ce ta ce su cire mata na'urar sai suka ce mata, 'da mun cire maki wannan, shikenan, Ba za ki daɗe ba'.

"Sai ta ce 'eh, na san haka, amma ya ishe ni'," in ji Mrs Sharma mai shekara 49.

"Mun samu mintuna biyar da ita a lokacin da take iya magana, sai daga baya ta fita hayyacinta.

"Ta bayyana mana cewa ba ta tsoron ta mutu, ta ce ta shirya mutuwa. Ta ce mani ya kamata na yaƙi cutar matuƙa saboda ina da yara a gida."

Anabel and Maria

Asalin hoton, Anabel Sharma

Ƴar uwar Mrs Sharma, Susana tana wurin da mahaifiyarsu ta mutu, amma tana sanye da kayan kariya.

"Mun riƙe hannunta har ta yi numfashinta na ƙarshe," a cewarta.

"Ina samun sauƙi a zuciyata idan na tuna cewa muna tare da ita kuma na san na ƙara wa mahaifiyarmu kwanciyar hankali".

Mrs Rico na zama a gida ɗaya da Mrs Sharma da mijinta da ƴaƴanta uku, Noah mai shekara 10 da Isaac mai shekara 12 da Jacob mai shekara 22.

Mrs Sharma ta bayyana cewa tana da yaƙinin cewa ɗaya daga cikin ƴaƴanta sun kamu da cutar korona a makaranta inda cutar ta bazu a cikin gidansu cikin sauri.

"Zan buƙaci mutane su ɗauki matakan kariya su kuma tuna da wasu," in ji ta.

Maria with her daughter and grandsons

Asalin hoton, Anabel Sharma

A rana ɗaya aka kai Misis Sharma da mahaifiyarta asibiti a watan Oktoba, inda Misis Rico ta mutu a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Mrs Sharma ta kalla jana'izar mahaifiyarta ta intanet yayin da take kwance a asibiti.

Maria at home

Asalin hoton, Anabel Sharma

"Tana sane da abin da zai faru da ita kuma ta san cewa ba zai ta warke ba, kuma an yi mata magani sosai," in ji Mrs Sharma wadda aka ci gaba da saka mata na'urar taimaka wa numfashi saboda da cutar ta taɓa mata huhu.

Ta bayyana mahaifiyarta a matsayin kaka mai kirki wadda take da ƙarfin hali.