Covid-19: 'Cutar korona ta kashe ƴan jarida 600 cikin watanni 10 a duniya'

..
An wallafa

Sama da ƴan jarida 600 ne annobar korona ta kashe a faɗin duniya cikin watanni goma da suka gabata.

Ƙungiyar nan mai zaman kanta ta Press Emblem Campaign da ke Geneva ce ta ruwaito hakan inda ta ce cutar ta rinƙa kashe aƙalla ƴan jarida 60 a wata, ko kuma mutum biyu a kowace rana.

Tun a watan Maris ɗin 2020 ne ƙungiyar ta ɗauki aniyar tattara bayanai dangane da ƴan jaridar da cutar korona ke halakawa, tare da wallafa sunayensu da taƙaitaccen bayani da hotunansu a shafinta.

Sakataren ƙungiyar ya jaddada cewa akwai ƴan jarida da dama da ba su iya aiki daga gida dole sai sun fita, kamar masu nemo rahoto da masu ɗaukar hoto da ƴan jarida masu zaman kansu inda akasarinsu suna kamuwa da cutar.

Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana cewa a ƙasashen da ke yankin Latin Amurla ne aka fi samun mutuwar ƴan jaridar, inda a nan kaɗai mutum 303 suka mutu cikin watanni goma.

Ƙasar Peru ta sanar da mutuwar ƴan jarida 93 sai kuma Brazil aka samu 55 da kuma Ecuador 42.

Sauran ƙasashen da suka bayar da rahoton mace-macen ƴan jarida sanadin korona sun haɗa da Indiya inda aka samu mutum 53 sai Mexico mutum 45 da Bangladesh mutum 41.

Haka kuma Italy ta bayyana mutuwar mutum 37 sai kuma Amurka 31. Sai dai ƙungiyar ta Press Emblem Campaign ta bayyana cewa waɗannan bayanan da ta tattara, ta same su ne daga majiyoyi daban-daban.

A cewarta, akwai yiwuwar ta rage adadin ƴan jaridar da suka mutu, sakamakon akwai wasu rahotannin ma da ba lallai ta same su ba.

An dai kafa wannan ƙungiya ne a 2004, inda ta mayar da hankali wurin kyautata tsaron ƴan jarida a faɗin duniya musamman a wuraren da ake rikice-rikice ko kuma wuraren da ke da hatsarin aiki.