Ƙayatattun hotunan wasu abubuwa da suka faru a sassan duniya a shekarar 2020

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotunan wasu abubuwan da suka faru a sassan duniya a shekarar da ta ƙare ta 2020.

A burnt paw of a brushtail possum is pictured as it is nursed by volunteers in Merimbula, Australia, 9 January 2020

Asalin hoton, Tracey Nearmy / Reuters

Bayanan hoto, Wani mai aikin sa-kai na duba wata dabba da ta kone a tafin kafarta a Merimbula, kasar Australia. A watan Yulin shekarar 2019 zuwa watan Maris na shekarar 2020, gobarar daji ta mamaye fadin kadada miliyan 24 million na kasar, tare da hallakawa da jikkata mutane da lalata gidajensu - har ma da hallaka da kuma haifarwa biliyoyin dabbobi rasa matsugunansu.
Film producer Harvey Weinstein arrives at New York Criminal Court for his sexual assault trial in the Manhattan borough of New York City, on 9 January 2020

Asalin hoton, Brendan McDermid / Reuters

Bayanan hoto, Harvey Weinstein ya isa kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta birnin New York, a cikin watan Janairu, don fuskantar tuhume-tuhume kan aikata fyade da cin zarafi ta hanyar lalata. An yanke wa shahararren mai shirya fina-finan 'Hollywood' na Amurkar hukuncin daurin shekaru 23 a gidan yari.
Italian alpine rescuers climb a frozen waterfall in Malga Ciapela, Italy, 11 February 2020

Asalin hoton, Yara Nardi / Reuters

Bayanan hoto, Masu aikin ceto ya yankin Alps sun hau kan daskararren ruwa mai kwaranya a Malga Ciapela, kasar Italiya, cikin watan Fabrairu.
Medical workers in protective suits attend to Covid-19 patients at an intensive care unit in Wuhan, Hubei province, China, 6 February 2020

Asalin hoton, China Daily via Reuters

Bayanan hoto, Ma'aikatan kiwon lafiya na duba masu dauke da cutar korona a dakin bayar da taimako gaggawa na musamman a birnin Wuhan, kasar China, cikin watan Fabrairu. Kwayar cutar wacce aka bayyana ta samo asali ne a wata kasuwar dabbobi a birnin, ta haifar da barkewar annobar da ta girgiza duniya.
An intensive care nurse takes a break in Brussels, Belgium, 24 April 2020

Asalin hoton, Stephanie Lecocq / EPA-EFE

Bayanan hoto, A birnin Brussels, wata ma'aikaciyar jinya a sashen bayar da taimakon gaggawa na musamman na hutun wucin gadi a yayin da ake cigaba da fuskantar barazanar annobar cutar korona.
Workers carry a coffin in a cemetery complex for coronavirus victims in Jakarta, Indonesia, 22 April 2020

Asalin hoton, Willy Kurniawan / Reuters

Bayanan hoto, An kawo makarar wani wanda cutar corona ta hallaka cikin makabarta a birnin Jakarta, kasar Indonesia. A karshen watan Aprilu ne, Jami'ar Johns Hopkins ta bayar da rahoton cewa adadin wadanda suka mutu a duniya da cutar ya wuce mutane 200,000.
A mother and daughter embrace through a plastic sheet in Wantagh, New York, on 24 May 2020

Asalin hoton, Al Bello / Getty Images

Bayanan hoto, Wata uwa da 'yarta na rungumar juna ta cikin jakar leda da aka tanada don kare su daga kamuwa da kwayar cutar korona a Wantagh, birnin New York. Kasashe a fadin duniya sun bullo da tsarin matakan kulle da kuma yin nesa da juna, don taimakawa wajen hana yaduwar cutar.
A man chases a swarm of desert locusts in Samburu County, Kenya, on 21 May 2020

Asalin hoton, Fredrik Lerneryd / Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na ta bin dandazon farin dango na cikin hamada a yankin Samburu, kasar Kenya, cikin watan Mayu.Biliyoyin kwari ne suka lalata amfanin gona a fadin kasashen Yammacin Afirka, bayan mamakon ruwan saman da ya haifar musu da yanayin da za su kara kyankyasa.
A man kneels in front of a memorial and mural for George Floyd

Asalin hoton, Joe Raedle / Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum ya durkusa a gaban babban zanen hoton tunawa da George Floyd a birnin Houston, jihar Texas. Mr Floyd ya mutu a cikin watan Mayu a Minneapolis, lokacin da wani dan sanda farar fata ya durkusa a kan wuyansa har na tsawon kusan minti tara, da hakan ya haifar da zanga-zanga a fadin kasar.
A competitor dives from Stari Most, also known as Old Bridge, on 26 July 2020, in Mostar, Bosnia and Herzegovina

Asalin hoton, Damir Sagolj / Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai gasar yin nutso daga Stari Most, da kuma ake kira 'Old Bridge', lokacin gasar wasan gargajiya na nutso karo na 454th a Mostar, a Bosnia da Herzegovina.
Men walk towards law enforcement with their hands up on 24 August 2020, in Kenosha, Wisconsin

Asalin hoton, Brandon Bell / Getty Images

Bayanan hoto, Wasu maza na tunkarar jami'an tsaro da hannuwansu a dage, a Kenosha, jihar Wisconsin. Zanga-zanga ta barke a watan Agusta, bayan da 'ya sanda suka bude wuta kan wani bakar fata, Jacob Blake, lokacin da suke mayar da martini kan abinda suka kira batun da ya shafi cikin gida.
A member of the Lebanese army walks past a wrecked grain silo at the site of a deadly blast in Beirut's port area, on 7 August 2020

Asalin hoton, Mohamed Azakir / Reuters

Bayanan hoto, Wani jami'in sojin kasar Lebanon na wucewa ta wajen ginin rumbun ajiyar kayan abinci da ya ruguje, bayan wani mummunan fashewa a yankin bakin ruwa na birnin Beirut. A zargi babban dakin ajiyar makare da kusan tan 3,000 na sinadarin 'ammonium nitrate' da haddasa fashewar da ta hallaka mutane fiye da 200, tare da jikkata sauran kusan 5,000 a cikin watan Agusta.
A woman embraces a member of the Belarusian interior troop near the Government House in Independence Square in Minsk, Belarus, 14 August 2020

Asalin hoton, Vasily Fedosenko / Reuters

Bayanan hoto, Wata mata ta rungumi wani jami'in sojin kasar Belarus, lokacin wata zanga-zanga a birnin Minsk. Zaben shugaban kasar na ranar 9 ga watan Agusta da zai bai wa dadadden shugaba Alexander Lukashenko damar sake yin tazarce duk kuwa da zargin da ake yi masa na magudin zabe, ya rura wutar zanga-zangar gagarumar zanga-zanga a kasar.
A woman takes in the view from the Embarcadero as smoke from various wildfires blankets San Francisco in darkness and an orange glow on 9 September 2020

Asalin hoton, Philip Pacheco / Getty Images

Bayanan hoto, A watan Satumba, hayakin gobarar daji mai ya turnuke birnin San Francisco cikin launin ruwan goro. Gobarar ta kone miliyoyin kadada a jihar ta California cikin wannan shekarar, tare da hallaka akalla mutane takwas.
US President Donald Trump speaks, with a flag behind him, during a campaign rally at Cecil Airport in Jacksonville, Florida, on 24 September 2020

Asalin hoton, Tom Brenner / Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Donald Trump na magana a lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a Jacksonville, jihar Florida. Mako guda kafin Amurkawa su fara gudanar da zaben, Mr Trump ya bayyana cewa shi da maidakinsa Melania Trump sun kamu da kwayar cutar korona.
Students wear protective face masks as they have their temperature checked before entering a class in Peshawar, Pakistan 23 September 2020

Asalin hoton, Fayaz Aziz / Reuters

Bayanan hoto, Dalibai a birnin Peshawar, kasar Pakistan, ana gwada zafin jikinsu kafin su shiga aji, bayan da gwamnati ta amince a sake bude makarantu a yayin da ake cigaba da fama da annobar korona.
Fires rage at the Moria migrant camp on 9 September 2020, in Lesbos, Greece

Asalin hoton, Byron Smith / Getty Images

Bayanan hoto, Gobara ta mamaye sansanin 'yan gudun hijira na Moria, a tsibirin Lesbos. Wutar da lalata sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a kasar Girka , da ta haifarwa da dubban mutane rashin matsugunai.
A woman takes a selfie as her friend adjusts her makeup in a pink muhly grass field in Hanam, South Korea, 13 October 2020

Asalin hoton, Kim Hong-Ji / Reuters

Bayanan hoto, Wata mata na daukar hoto salon dauki kanka da kanka 'selfie' a cikin wata gonar ciyayi masu launin ruwan hoda a yankin Hanam, kasar Korea ta Kudu cikin watan Oktoba.
US presidential nominee Joe Biden and his wife Jill, and vice presidential nominee Kamala Harris and her husband Doug, in Wilmington, Delaware, 7 November 2020

Asalin hoton, Jim Bourg / Reuters

Bayanan hoto, Dan takarar shugabancin Amurka Joe Biden na mayar da martini lokacin gangamin yakin neman zabe a Wilmington, Delaware, bayan da kafafen yada labarai suka bayyana nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa na shekarar 2020. Jam'iyar Democrat ta samu galaba a kuri'un wakilan 'lectoral college' da kuri'u 306 kan Jam'iyar Republica ta Donald Trump da ta samu kuri'u 232.
A metro train rests precariously on an art installation of a whale in Spijkenisse, near Rotterdam, Netherlands, 2 November 2020

Asalin hoton, Eva Plevier / Reuters

Bayanan hoto, Wani jirgin kasaa a birnin Spijkenisse, a kasar Netherlands, a shinfide kan wani katon mutum-mutumin kifin 'whale' bayan da ya yi hatsari ta cikin karshe titinsa. Gunkin kifin ne ya yi wa jirgin kasar garkuwa daga abkawa cikin kogin da ke kasansa mai zurfin mita 10 (kafa 32), kana direban ya tsira ba tare da jin ciwo ba.
A man covered in mud in San Mateo, Rizal province, Philippines, 13 November 2020

Asalin hoton, Eloisa Lopez / Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum na hutun wucin gadi daga share gidansa, bayan ambaliyar ruwan da mahaukaciyar guguwar teku Vamco ta haddasa a San Mateo, kasar Philippines. Mahaukaciyar guguwar ta watan Nuwamba it ace irinta ta 21 da ta abka wa kasar a cikin wannan shekarar, tare da hallaka gwamman mutane.
A demonstrator paints the helmet visor of a riot police officer, in Mexico City, Mexico, 11 November 2020

Asalin hoton, Toya Sarno Jordan / Reuters

Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga na yi shafa jan fenti a gaban hular kwanon wani jami'in dan sandan kwantar da tarzoma a birnin , lokacin wata zanga-zanga nuna jin cijin cin zarafin jinsi a kasar.
Refugees from the Tigray region of Ethiopia wait to be transferred to a camp

Asalin hoton, Byron Smith / Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan gudn hijira daga yankin Tigray na kasar Ethiopia na jiran a kwashe su zuwa sansanin 'yan gudun hijira na kasar Sudan makwabciya. Tun a ranar 4 ga watan Nuwamba ne, aka bayyana mutuwar daruruwan mutane a wani artabu tsakanin dakarun kasar ta Ethiopia da na kungiyar masu rike da makamai na yankin Tugray (TPLF), yayin da kusan 50,000 suka tsere zuwa kasar ta Sudan.
A capsule from Japan's Hayabusa-2 space probe streaks through the night sky

Asalin hoton, Morgan Sette / AFP

Bayanan hoto, Kumbo daga tashar lura da sararin samaniyar kasar Japan Hayabusa-2 na tashi ta cikin sararin samaniya kafin ya dira a kusa da yankin Woomera a Kudancin Australia. Jirgin sama jannatin ya debi wasu duwatsu daga duniyar saman kafin ya dawo da samfurin zuwa doron duniyar kasa a cikin watan Disamba.

Dukkan hotunan suna da haƙƙn mallaka.