Kaduna sex party: Yadda gwamnati ta hana dabdalar nuna tsiraici

Kaduna sex party

Asalin hoton, Abdul85/Twitter

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƴan sanda a Kaduna sun damƙe wasu matasa da suka yi niyyar haɗa wata dabdala ta nuna tsiraici wadda aka yi ta tallatawa a shadfukan sada zumunta baya-bayan nan.

An yi niyyar yin wannan dabdalar a ranar 27 ga watan Disamban 2020 kafin gwamnatin jihar Kaduna ta daƙile yunƙurin matasan.

Waɗanda suka shirya wannan dabdalar, sun buƙaci mahalarta bikin su je wurin tsirara.

Mai taimaka wa gwamnatin jihar Kaduna kan kafofin watsa labarai, Abdallah Yunus Abdallah ne ya tabbatar wa BBC da batun kama waɗanda suka yi niyyar shirya wannan ƙwarya-ƙwaryar bikin.

"Lambar da suka saka kan takardar gayyata, ita aka yi amfani wurin gano waɗanda suka shirya dabdalar kuma a yanzu an kama su," in ji shi.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi yunƙurin gudanar da irin wannan dabdalar a bayyane a arewacin Najeriya.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Mohammed Jagile ya tabbatar wa BBC da wannan lamarin inda ya ce daga nan gaba kaɗan zai yi ƙarin bayani a kai.

Me mutane ke cewa kan wannan dabdalar?

Batun wannan dabdalar ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da aka rinƙa tattaunawa a ƴan kwanakin nan musamman a shafukan sada zumunta.

Mutane da dama sun yi zaton batun wannan dabdalar wasa ne kawai, ko kuma irin tsokana ce da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, sai da suka ji labarin cewa gwamnatin jihar ta kama waɗanda suka shirya bikin tukuna suka yarda da gaske ne.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wannan cewa ya yi ya kamata a kama waɗanda suka shirya "wannan lalatar".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan kuma cewa ya yi "wasu sun haɗa dabdalar tsiraici a jiya a Kaduna cikin wannan lokaci na korona, mutane ba su da tsoro", in ji shi.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wannan kuma cewa ya yi "me al'ummar mu ke son komawa?" Ya kuma roƙi Allah Ya shirya waɗanda suka shirya wannan dabdalar da kuma waɗanda suka yi niyyar halartar wurin.