Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: An bayar da belin matar da ake zargi da kashe 'ya'yanta
An bayar da belin matar da ake zargi da kashe ƴaƴanta biyu a Kano a kwanakin baya.
An bayar da belin nata ne kan dalilan rashin lafiya amma duk da hakan kotu ta ce za a rinƙa kai ta asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyarta da sanar da kotu halin da take ciki.
Lamarin wanda ya faru tun a watan Oktoba a Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa saɓani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.
Amma daga baya mahaifiyar matar da mijinta sun ce ta daɗe tana fama da rashin lafiya mai nasaba da iskokai kuma tana nuna alamun hakan.
Ta kuma shaida cewa tun da ta aurar da ƴarta shekara shida da suka gabata, ƴarta take tafka rikici da mijinta. "Kullum faɗa suke da mijinta," in ji uwar matar.
A halin yanzu dai lauyoyin matar da ake zargin ne suka nemi belinta, kuma tana asibitin Aminu Kano a ɓangaren duba lafiyar ƙwaƙalwa.
Haka kuma za ta ci gaba da bayyana a gaban kotun majistare da ke Gidan Murtala.
Tun a lokacin da lamarin ya faru, BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma'ana mijin matar da ake zargi da kashe ƴaƴan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhini da yake ciki sakamakon abin da ya faru.
Lamarin dai ya ɗauki hankulan jama'a da dama musamman ganin irin shaƙuwar da ke tsakanin ɗa da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi ba zai sa uwa ta hallaka ƴaƴanta ba, don haka mutane ke fatan samun sahihiyar amsa bayan kammala shari'ar da ake yi mata.