Matar da ta kashe 'ya'yanta a Kano: Shin matsalar ƙwaƙwalwa ce ko shafar aljanu?

An wallafa

Labarin matar da ta kashe 'ya'yanta biyu a unguwar Sagagi da ke birnin Kano a Najeriya na cigaba da jan hankali da diga ayar tambaya kan yanayin lafiyarta.

Da farko an bayyana cewa lamarin ya faru ne kan sabanin da ta samu da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu amma daga baya wasu bayanai daga iyayenta na cewa shafar aljannu ce.

Tun bayan kisan wadannan yara biyu yan shekara biyar da uku ake ta samu mabambanta ra'ayi kan dalilan da zai kai ga uwa ta kashe yayanta da hannunta.

Har yanzu dai hukumomin 'yansanda na kan bincike domin tabbatar da gaskiyar yada wanann lamari ya faru

Wace ce mahaifiyar wadannan yara?

Matar da aka bayyanan sunanta da Hauwa'u Habib tana da shekaru tsakanin 24 zuwa 25.

Tana aure a Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya a birnin Kano, da 'ya'yanta 2 sai 'yar riko guda.

Iyayenta sun ce ta shafe tsawon wata uku ba ta iya bacci, "tana cewa kullum cikin dare ana zuwa ana danne ta ana shake ta.

Ta fi wata uku ba ta bacci, da dare ana yi mata gurnani irin na dodanni."

Da farko ba su ɗauki maganarta da muhimmanci ba amma sun fada mata cewa ta dinga yin addu'a kuma ta fada wa mijinta.

Mahaifiyar ta ce tun da ta aurar da ƴarta shekara shida da suka gabata, take tafka rikici da mijin.

Mahaifiyar ta kuma ce daga baya ƴarta ta samu rashin lafiyar, kuma ƴarta ta taba zuwa wurin malami har aka yi mata karatu amma rashin lafiyar ta kara tsanani.

Mijin Hauwa'u, da aka bayyana sunansa da Ibrahim Haruna Aminu ya ce dama a wasu lokutan ta kan fita daga hayacinta.

Domin ko kafin kashe yaranata ta sha bayyana cewa tana ganin wasu abubuwa.

Ita kanta Hauwa'u ta ce tana yawan ganin ana binta, wasu lokutan tana jin gudu a kafar bene, ko idan ta kashe fitilar kwai sai ta ga an kunna.

Sannan ta bayyana cewa ta kashe yaran nata ne sakamakon bin ta da taga sun yi da wuka, kuma harta shi kansa mijin yana sauya mata wani lokaci sai ta ganshi da kofato.

Diyar da Hauwa'u take riko Aisha mai shekara 10 ta bayyana cewa dama ta jima tana tsoronta saboda a wasu lokutan ta kan bi ta da gudu.

Aisha ta ce ko lokacin da Hauwa'u ke kokarin aikata kisan babu alamar ta gane 'ya'yanta domin tana ambatarsu da musu kallon wasu na daban.

Wane hali ake ciki yanzu?

Magana dai tana gaban 'yansanda kuma har yanzu ana bincike domin gano gaskiyar yadda ta aikata hakan.

Haka kuma ƴan sandan za su yi bincike kan mijin domin gano ko yana da hannu a aikata kisan.

Shimfida

A ranar Asabar ne rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma biyar da ake zargin mahaifiyarsu ce ta kashe su.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami'anta sun kama matar yanzu haka tana hannunsu, kuma ta tabbatar da cewa ita ta kashe ƴaƴanta.

Lamarin ya daure wa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musamman makwabtan gidan da lamarin ya faru, inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar ba ta da tabin hankali haka kuma ba a san ta da shaye-shaye ba.

Sharhi - Umaymah Sani Abdulmumin, BBC Abuja

Mutane da dama sun kadu da samun wannan labari, wasu ma tunaninsu shi ne cikakkiyar lafiyar wannan mata.

Akwai wadanda ke ganin akwai batun rashin bai wa duba lafiyar kwakwalwa muhimmaci da ya taka rawa a wajen kisan wadanan yara da mahaifiyarsu tayi.

A galibin lokutan idan aka fahimci mutum na da matsala ko yawan fita daga hayaci akan danganta hakan da shafar aljannu da kin zuwa asibiti ko duba lafiyar kwakwalwa.

Bincike ya nuna cewa akwai mutane da dama da ke fama da matsalar kwakwalwa ko damuwa ba tare da sun sanii ba.

Sai dai watakil abin da Hauwa ta aikata akan yaranta ya sake ankarawa da muhimmanci sa ido kan yanayin mutane, halaya da dabi'u.

Karin labarai da za ku so ku karanta: