Rikicin Darfur: Dalilin da ya sa Abdullah bai taɓa zuwa garinsu ba

.
An wallafa

A daidai lokacin da dakarun wanzar da zaman lafiya a Sudan ke shirin barin yankin Darfur da yaƙi ya ɗaiɗaita, ana ta samun fargaba kan yadda tsaron farar hula zai kasance idan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma ta wargaje, kamar yadda wakilin BBC Mike Thomson ya ruwaito.

Abdullah yaro ne ɗan shekara 14 kuma yana zaune kan wata tsohuwar taya a gaban wata lalatacciyar bukka da aka yi saboda 'yan gudun hijira.

An haife shi a Abu Shouk da ke wajen birnin Fasher na Arewacin Darfur, wurin da ya shafe akasarin shekarunsa - kuma da wayonsa, bai taɓa zuwa ƙauyen da iyayensa ke ambata a matsayin gidansu ba.

"An ba ni labari cewa iyayena da sauran dangina a baya na zaune a wani ƙauye mai kyau da ke zagaye da gonaki.

"Iyayena sun shaida mani cewa ƙauyen wuri ne mai kyau kuma rayuwa ta fi dadi a can."

Abdullah ya taɓa ganin talabijin sau ɗaya a rayuwarsa, kuma a kullum yana cikin fargaba sakamakon 'yan fashi da wasu lokuta kan kai hari a sansanin da dare.

..

"Muna ɓuya, babu wani abin da za mu iya yi. Idan mutum ya ce zai yi fada da su, za su far masa."

Ana sa ran wannan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a 'yan kwanakin nan za ta bai wa Abdullah damar komawa garinsu, da kuma kawo ƙarshen rikicin da aka ɗauki shekara 17 ana gwabzawa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 300,000 da kuma tilasta wa mutum miliyan 2.5 barin gidajensu.

Map of Sudan
1px transparent line

Rikicin ya fara ne tun a 2003, a lokacin da wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suka yi tawaye ga gwamnatin ƙasar, inda suke zargin cewa an yi watsi da yankinsu.

Gwamnatin Khartoum, babban birnin ƙasar, ta mayar da martani ta hanyar bai wa Larabawa makiyaya makamai, waɗanda daga baya suka gawurta suka zama ƙungiyar Janjaweed, inda ake biyan su domin su kwantar da tarzoma, inda suke nuna rashin imani yayin kwantar da tarzomar.

A halin yanzu, ƙungiyoyin 'yan tawaye da dama a Sudan sun saka hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin ƙasar, amma duk da haka akwai mutum aƙalla miliyan 1.5 kamar Abdullah da ke sansani kusan 60 a yankin Darfur.

Amma mutane da dama kamar Zara, wadda ta shafe shekara 17 a sansanin Abu Shouk, ta ƙosa ta koma gida, amma ta kasa.

"Ba za mu iya komawa gonakinmu ba sakamakon wasu sun ƙwace su. Su ne suka kashe mu, su ne suka kore mu, mu kuma har yanzu muna nan."

Kullum kisa ake yi

Tafiyar da muka yi zuwa garin Nertiti, kusan tafiyar sa'o'i shida a mota daga sansanin Abu Shouk, ta ƙara fito da wasu abubuwa da suka zama dalilan da suka sa 'yan gudun hijira da dama ba za su so su koma gidajensu ba.

Manoma da dama a garin na tsoron komawa gonakinsu sakamakon kashe-kashe da fyaɗe da ake yi

Su kansu da ke cikin garin suna cikin hatsari matuƙa.

A kwanakin baya ne ƙungiyar Janjaweed ta kashe mijin Khadiga Ishaq da ɗanta ɗaya kafin su harbe ta a gidansu da ke Nertiti.

"Kullum rikici ake yi, kullum kisa ake yi," in ji ta.

"Ba mu yarda da gwamnatinmu ba, da sojoji da 'yan sanda, ba mu yarda da su ba. Idan ba a samu mafita ba za a yi kisan ƙare-dangi a nan."

.

Dalilin da ya sa Khadiga da sauran jama'a ke tsoron sojoji shi ne, akwai da dama daga cikin sojojin waɗanda a baya mayaƙan Janjaweed ne waɗanda suka addabe su.

Ba wannan kaɗai ba, a ƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyan da aka saka wa hannu, za a saka wasu daga cikin mambobin 'yan tawaye a cikin sojojin Sudan.

A ƙarshen Disambar nan, dakarun zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya za su janye daga Sudan bayan shafe kusan shekara 13.

Duk da cewa wannan haɗakar ta sojojin MDD ba ta bayar da wata gudunmawar a-zo-a-gani ba wurin kare rayukan farar hula, ana ganin cewa zamansu ya taimaka matuƙa wajen daƙile cin zarafin da sauran dakaru ke yi.