Kotun Ƙolin Amurka ta ƙi amincewa Shugaba Trump ne ya lashe zaɓe

An wallafa

Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da wata ƙara irin ta ta farko a tarihi da Shugaban ƙasar Donald Trump ke mara wa baya, wadda aka buƙaci Kotun Ƙolin ta sauya sakamakon zabukan da aka yi a jihohi huɗu da Trump ya faɗi zaben shugaban ƙasa.

An dai shigar da ƙarar ne a jihar Texas, kuma jihohin da wadanda suka shigar da ƙarar suka nemi a soke sakamakon zabukan su ne Georgia da Michigan da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Joe Biden ne ya lashe zaɓukan da aka yi a duka jihohin huɗu.

Ƴan majalisar Amurka daga jam'iyya mai mulki ta Republican su 127 tare da lauyoyin gwamnatocin jihohi 19 sun goyi bayan wannan ƙarar.

Amma Kotun Ƙolin ta yanke hukunci tana cewa jihar ta Texas ba ta da hurumi a shari'ance na shigar da irin wannan ƙarar, kuma ta yi watsi da ƙarar nan take.

"Jihar Texas ta kasa nuna wa a shari'ance yadda wannan zaben ya shafe ta ganin cewa kowace jiha tana da ikon gudanar da zaɓuka a ƙarƙashin dokokinta," inji Kotun Ƙolin.

Wannan hukuncin ya kasance wani gagarumin koma-baya ga Mista Trump, wanda a baya ya kafe cewa sakamakon zaben shugaban Amurka na watan Nuwamba an tafka magudi a cikinsa.

Mista Trump ya sha yin iƙirari cewa "ƙuri'un bogi" ne su ka kayar da shi a ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da samun wa'adi na biyu na mulkinsa.

Tun bayan da aka gudanar da zaben, Mista Trump da magoya bayansa sun shigar da gomman ƙararraki wadanda a ciki su ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen. Babu ko guda ɗaya da ta goyi bayan masu shigar da ƙarar.

Dan takarar da jam'iyyar adawa ta Democrat ta tsayar, Mista Joe Biden ya sami ƙuri'u 306, inda shi kuma Mista Trump ya sami ƙuri'u 232 na kwamitin masu zaɓe da ake kira Electoral College.

Wadannan mambobin kwamitin masu zaben ne ke zaben shugaban ƙasa.

Ban da wannan tazarar, Mista Biden ya lashe zaben da ƙuri'u fiye da miliyan bakwai idan aka kwatanta da wadanda Mista Trump ya samu na adadin masu zabe da suka fita ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin zaben shugaban da zai jagoranci Amurka na shekara hudu mai zuwa.

Ranar Litinin mai zuwa ne kwamitin masu zaɓen za su taru a birnin Washington domin tabbatar wa Joe Biden cewa shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 3 ga watan Nuwamba, 2020.