Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EndSars: Shin zanga-zangar EndSars ta dawo ne?
Ɗumbin mutane ne suka fantsama a kan titunan Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya a ranar Litinin domin gudanar da zanga-zanga don neman yin garanbawul ga harkokin 'yan sandan ƙasar.
Zanga-zangar, wadda aka yi wa laƙabi da EndSars, ta fara ne a watan Oktoba, sakamakon cin zalin da ake zargin 'yan sanda suna yi ne ko da yake ta rikide zuwa tarzoma.
Hotuna da bidiyon da masu gangamin suka riƙa wallafawa a shafukan sada zumunta ranar ta Litinin sun nuna masu zanga-zangar suna yin tattaki a kan titunan Legas
Suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu daban-daban ciki har da kira ga hukumomi su ba su damarsu ta zama 'yan ƙasa.
A Legas ɗin, rahotanni sun nuna cewa an jibge jami'an tsaro a sassan daban-daban na birnin bayan hukumomi sun yi gargaɗin cewa ba za su bari a koma yin zanga-zangar ta #EndSARS ba.
A ranar Lahadi ne rundunar 'yan sandan jihar ta fitar da sanarwar da ta hana gudanar da zanga-zangar, tana mai gargaɗin cewa duk wani mataki na sake yin zanga-zangar zai gamu da fushinta.
Zanga-zangar da aka yi a baya a jhar ta Legas da ma wasu jihohi ta haifar da ƙone-ƙone, inda a Lagos kaɗai aka yi asarar fiye da naira biliyan 400.
Me masu zanga-zangar ke cewa?
Tun da safiyar Litinin ne aka fara tattauna mau'du'in EndSars a Twitter inda har ya zama ɗaya daga cikin manyan mau'du'an da aka tattauna a ranar.
Wannan cewa ta yi an soma guguwar zanga-zangar #EndSARS karo na biyu inda ta ce kar a ce komai, a ci gaba da rarraba saƙon.
Wannan kuma cewa ya yi an ci gaba da gudanar da zanga-zangar EndSars a karo na biyu, tuni mutane suka hau tituna, in ji shi.
Me gwamnatin Najeriya ke cewa?
A ranar Litinin ne Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Twitter inda ya gargaɗi masu shiga rigar masu zanga-zangar lumana domin jawo hargitsi inda ya ce lallai za su ɗanɗana kuɗarsu.
Shugaban ƙasar ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda zanga-zangar ta EndSars a kwanakin baya ta jawo rasa rayuka da kuma asarar dukiyoyi a faɗin ƙasar.