An sallami 'yan sandan Najeriya 17 an rage wa 18 muƙami

An wallafa

Rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta sallami jami'anta goma sha baƙwai da kuma bai wa wasu da dama takardun gargaɗi da kuma horo na gwale-gwale.

An samu ƴan sandan da aikata ba daidai ba da suka haɗa da kisan kai da kuma wuce gona da iri.

Sanarwar da rundunar ƴan sanda ta jihar Legas ta fitar wadda ta aike wa BBC, ta ce wannan mataki da ta ɗauka, wani ƙoƙari ne na inganta tarbiyya da kyawawan ɗabi'u na ƴan sanda a jihar Legas.

Rundunar ta yi wa ma'aikata 81 shari'a kan laifuka daban-daban na ladabtarwa da suka aikata tsakanin watan Oktoba na shekarar 2019 da watan Oktoba na shekarar 2020, ciki kuwa har da sallamar ƴan sanda 17 daga bakin aiki, bayan an same su da aikata ba dai-dai ba.

Laifuffukan da aka tuhume su dai sun haɗa da na kisan kai da ayyukan rashin gaskiya da wuce gona da iri da amfani da ƙarfi da yin sakaci a yayin da suke bakin aiki.

Sanarwar wacce Olumuyiwa Adejobi, babban jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sanda a jihar ta fitar ta ce rundunar ta kuma tuhumi wasu jami'ai bakwai tare da gurfanar da su a gaban shari'a, yayin da aka kori ma'aikata 17, kuma takwas daga cikinsu maza ne.

Haka nan kuma an rage wa ƴan sanda maza 18 muƙami. Ta ce akwai wasu 29 da aka ba su takardun gargaɗi domin su gyara halayensu. Wasu kuma an ba su horo na gwale-gwale.

Sai dai an wanke wasu ƴan sanda 16 daga laifuffukan da ake zarginsu akai, sakamakon rashin hujjoji ƙwarara.

Muƙaman ƴan sanda da abin ya shafa

Ma'aikatan da aka yi wa shari'ar ɗaya bayan ɗaya sun zo bayan aikata laifuffuka a wurare daban-daban a cikin jihar Legas.

Ƴan sandan sun haɗa da Sufeto da kofur-kofur. Haka nan an samu wasu manyan jami'an ƴan sanda da laifuka daban-daban na ladabtarwa kuma ana ci gaba tuhumarsu a babban ofishin rundunar ƴan sanda da ke a Abuja domin ɗaukar matakan da suka dace.

Yan sandan da aka miƙa sunayensu dai, ana zarginsu da aikata ba dai-dai ba a yayin da suke aiki a rundunar ƴan sanda da ke jihar Legas.

Wannan mataki da rundunar ta ɗauka dai ya zo a daidai lokacin da ake gabatar da ƙorafe-ƙorafe bisa zargin da ake yi wa ƴan sandan da ke yaƙi da ƴan fashi da makamai da kuma masu yi wa al'ummar ƙasa zagon ƙasa.

Abin da bai fito fili ba shi ne ko wannan sallama da ladabtarwa na cikin umarnin da Shugaba Buhari ya bayar domin duba al'amura da suka shafi ayyukan jami'an rundunar.

A baya-bayan nan ne wasu ƴan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar lumana da ta rikiɗe ta koma ta lalata dukiya da kisa, bayan sun nemi a rushe rundunar ƴan sanda ta SARS wanda gwamnatin tarayya ta yi, amma duk da haka zanga-zangar ta ci gaba da ta janyo hallaka rayuka da ɓarnata dukiya mai tarin yawa.

Dama gwamnatin jihar Legas ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi wanda ya fara zama domin gudanar da bincike bisa zargin da ake yi wa rundunar ƴan sanda ta SARS na wuce gona da iri kan jama'a da suke zargi masu aikata laifi ne.