Ƴan adawa a Nijar sun yi watsi da kasafin kuɗin 2021

An wallafa

Majalisar dokokin Nijar ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2021, sai dai ɓangaren ƴan adawa a majalisar sun yi watsi da shi.

Da ƙuri'a 130 daga cikin ƴan majalisar 150 da suka halarci zaman majalisar, kasafin kuɗin na 2021 ya samu amincewar wakilan al'ummar Nijar ɗin.

An dai kwashe tsawon yini guda ana tafka muhawara a kan kasafin kuɗin da gwamnati ta gabatarwa majalisar wanda ta yi akan cefa miliyan dubu ɗari biyu da ɗari shida da arba'in da huɗu da digo hamsin da uku.

Kasafin na 2021 dai ya haura na 2020 da cefa miliyan dubu ɗari da talatin da ɗigo goma sha huɗu.

To sai dai kuma ƴan adawa a majalisar sun jefa ƙuri'ar ƙin amincewa da kasafin kamar yadda daya daga cikinsu ya shaida wa BBC dalilinsu.

Honourable Sumana Hassan, shugaban gungun jam'iyyu masu adawa na Model Lumana, ya ce, sun jefa kuri'ar ƙin amincewa da kasafin na 2021 ne, saboda sun lura cewa gwamnati mai ci ta Muhammadou Issufou ba su sanya buƙatun al'umma suke sawa a gaba ba.

Ya ce: "Abin da suke sanyawa gaba shi ne muradun kansu, ma'ana suna son rai da kuma nuna ƙasaita a ciki, shi yasa muka yi watsi da shi".

Gwamnatin Nijar ta gabatarwa majalisar dokokin kasafin ne a yayin da aka shiga watan da za a gudanar da babban zaben ƙasar.

Yanzu haka shirye-shiryen zabubbuka masu zuwa sun kankama, baya ga na hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta CENI, jam'iyyu da 'yan takara na ci gaba da shirya taruka don ganawa da magoya bayansu.

Kawo yanzu dai 'yan takara daga jam'iyyun siyasa daban-daban 12 ne suka bayyana kansu don neman kujerar shugabancin kasar a zabubbukan da za su gudana.