Adam King: Yaro ɗan shekara shida da ke da burin aiki da 'yan sama jannati ya burge NASA

An wallafa

Wani yaro ɗan shekara shida wanda ya burge mutane da dama da ke da burin aiki da masu zuwa sararin samaniya ya ja hankalin hukumar da ke bincike kan sararin samaniya wato NASA.

Tun da farko dai, an ga Adam King a wani shirin yara na talabijin inda ya bayyana cewa yana so ya yi aiki tare da 'yan sama jannati idan ya girma.

Yaron, wanda ke da matsala ta naƙasa, ya samu saƙonni sosai daga manya ko kuma sanannun 'yan sama jannati da kuma hukumomin da ke bincike kan sararin samaniya na Amurka.

Hukumar NASA a shafinta na Twitter ta wallafa cewa "mun ƙagara ya zama ɗaya daga cikinmu wata rana".

Adam na daga cikin waɗanda aka gayyata a wani shiri na musamman na Kirisimeti.

Shirin dai, shiri ne na musamman da ake gudanarwa a duk shekara inda ake gayyatar yara daga gidaje daban-daban domin yin sharhi kan kayayyakin wasan da aka ƙera na baya-baya.

Sai dai Adam a wannan shekarar ya zama zakara bayan ya yi magana dangane da burinsa na zama ɗan sama jannati.

"Me kake so ka zama idan ka girma?" in ji mai gabatar da shirin Ryan Tubridy.

"Capcom a Nasa," in ji Adam.

Capcom dai wata kalma ce da 'yan sama jannatin ke amfani da ita da ke nufin mutumin da ke taimakawa wajen magana tsakanin 'yan sama jannati da kuma waɗanda ke nan duniya.

"Kana so ka zama ɗan sama jannati a nan gaba?" in ji mai gabatar da shirin

"Ni ba zan iya zama ɗan sama jannati ba saboda irin naƙasar da nake da ita," in ji Adam inda ya ce yana so ya yi aiki da waɗanda ke magana da 'yan sama jannati daga nan duniyar.