Coronavirus: An dauki sabbin matakai a Jamhuriyar Nijar

An wallafa

Ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Nijar ta sanar da ɓullo da wasu sabbin matakai da za su taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da bazuwar annobar korona wadda ta sake kunno kai a ƙasar.

Daga jibi Juma'a, duk fasinjan da ya sauka a filin jirgin saman ƙasar daga ƙasashen waje, ya zama dole ya killace kansa tsawon kwanaki.

A hirar da ya yi da BBC, ministan lafiya na Jamhuriyar Nijar Dr Idi Illiassou Mainasara ya bayyana cewa daga cikin sabbin matakan sun hada da tantance takardar cewa ya yi gwajin cutar daga kasar da ya fito da bai wuce kwana uku da yi ba.

Bayan haka Dr Idi Illiassou Mainasara ya ce 'zai killace kan shi gidan shi har tsawon sati guda'.

Ministan ya kara da cewa 'idan a ka tabbatar bai dauke da cutar Korona za a bashi fasfo dinshi,'

A cewar ministan idan kuma a ka gano cewa ya kamu da cutar to za a kula dashi tare da yi masa magani kyauta.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da adadin masu kamuwa da cutar Korona ke dada karuwa a Jamhuriyar Nijer, inda mutun sama da 1,000 su ka kamu, yayin da cutar ta kashe sama da mutun 80.

To sai dai a baya ministan lafiyar ya ce mutanen da suka rasu akasarinsu wadanda dama ba su da lafiya ne, da ke fama da matsalar zuciya da huhu da ciwon suga.