'Yan Twitter sun fusata kan yunƙurin ba jami'an Road Safety bindiga a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

'Yan Najeriya da dama sun fusata a shafukan sada zumunta musamman a Twitter tun bayan ɓullar wani labari da ake yaɗawa kan cewa za a fara bai wa jami'an hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya bindigogi.

Jaridar Daily Post a Najeriya ta ruwaito shugaban kwamitin hukumar ta FRSC a Majalisar Wakilai, Akinfolarin Mayowa, inda ya ce ya zama tilas a yi hakan domin tabbatar da an bi doka da oda.

Ya bayyana hakan ne yayin da hukumar ta hallara gaban kwamitin na majalisar domin kare kasafin kuɗinta na 2021 da ta gabatar.

Ya kuma ce kwamitin zai zauna da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha kan wannan batu, da kuma rubuta wasiƙa ga Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari domin aiwatar da buƙatar.

Me 'yan Najeriyar ke cewa?

Wannan yunƙurin na majalisar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke farfaɗowa daga rikicin da aka yi a wasu jihohi da masu zanga-zanga kan kawo ƙarshen rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

Da dama 'yan ƙasar a shafukan sada zumunta na da ra'ayin wannan yunƙurin na bai wa jami'an bindigogi tamkar dawo da rundunar SARS ɗin ne a fakaice.

Tun a jiya ake tattauna wannan batu a shafin Twitter ga kuma abin da wasu da suka bayyana ra'ayoyinsu ke cewa:

Wannan cewa ta yi wannan abin da za a yi tamkar sake kafa wata rundunar SARS ɗin ne. A cewarta, me waɗannan jami'an za su yi da bindiga? Ta ce ko a wasu ƙasashen Afrika, jami'an hukumar kiyaye haɗura na amfani ne da kimiyya wajen kama masu laifi da kuma hukunta su.

Wannan shi kuma cewa ya yi a ganinsa jami'an su riƙe bindiga ba laifi ba ne, amma ya kamata a horar da su ne kawai kan riƙe bindiga ƙirar Pistol ba wai AK47 ba, domin a cewarsa, gwamnatin Najeriya ba bindigar da ta sani sai AK47.

Wannan kuma cewa ta yi "hakan ba daidai ba ne, aikinsu ba shi ne riƙe bindiga ba, mene ne haɗarin da ke tattare da tabbatar da ba a yi gudu a hanya ba ko kuma duba takardun direba da kuma tabbatar da cewa ba a yi wa mota lodi ba? ya kamata Majalisar Wakilai ta sake tunani kan wannan lamari ko kuma akwai matsala".

Shi kuma wannan cewa ya yi shugaban hukumar ta FRSC ya bayyana cewa an sha samun direbobi na yi wa jami'an hukumar barazana.

A cewarsa, suna tsoron barazanar direbobi marasa bindiga ne, shi ya sa suke son su riƙe bindiga.

Ƙarin Bayani

BBC ta tattauna da wani daga cikin jami'in hukumar kuma ya tabbatar mana da yunƙurin majalisar na ɓukatar a bai wa jami'an hukumar ta FRSC bindigogi.

Ya ce tuni dama dokar da ta kafa hukumar a 1992 ta bayar da dama ga jami'an su riƙe makami, hakan ya sa ake so a amince a yanzu, in ji shi.

Sau da dama dai an sha tayar da irin wannan magana ta cewa za a bai wa jami'an na FRSC bindigogi, amma daga baya sai maganar ta yi shiru.