Katsina: Soja ɗaya ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa

Makaman 'yan fashi a Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto, 'Yan fashin sun kai hari a garin Faskari da misalin ƙarfe 5:30 na asuba
An wallafa

Wani sojan Najeriya ya rasa ransa lokacin da dakarun rundunar Operation Sahel Sanity suka kai wa 'yan fashi hari, inda suka ceto mata masu shayarwa guda uku tare da jariransu a Jihar Katsina.

Sojojin, sun yi nasarar kashe uku daga cikin 'yan fashin a fafatawar da aka yi ranar Alhamis da ta gabata, a cewar wata sanarwa da Muƙaddashin Daraktan Yaɗa Labarai, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ya fitar.

A cewar sanarwar, sojojin sun kai ɗauki ne bayan an shaida musu cewa 'yan fashin sun kai hari a ƙauyen Diskuru da ke Ƙaramar Hukumar Faskari da misalin ƙarfe 5:30 na asuba a kan babura, inda suka kashe mutane da dama.

Dakarun rundunar sun yi nasarar daƙile harin tare da raunata da yawa daga cikinsu.

"Bayan fafatawar, an ceto mata tare da yaransu waɗanda 'yan fashi suka yi garkuwa da su," in ji Bernard Onyeuko.

An gano ƙarin gawa biyu ta 'yan fashi biyu a kan hanyarsu ta guduwa, a cewarsa.

Sai dai ya ce wani soja da ya yi ƙoƙarin tserar da ɗaya daga cikin matan da aka yi garkuwar da su ya rasa ransa yayin fafatawar.

Sojojin sun ci gaba da kasancewa a garin bayan korar 'yan fashin domin tabbatar da tsaro a yankin da kuma maƙwabtansa.

Kakakin 'Yan Sanda na Jihar Katsina, SP Isah Gambo, ya tabbatar da cewa mutum 17 ne suka mutu jumulla. Huɗu daga cikinsu dakarun sa-kai ne, da 12 kuma mazauna ƙauyen ne, a cewar gidan talabijin na Channels.