Ƴan fashi a Katsina: ‘'Yadda ƴan bindiga suka yi wa mata shida fyaɗe a gabana’

Musa Adamu da ke zaune a ƙauyen Mallamawa ya tsere daga hannun ƴan fashin da suka sace shi bayan ya shafe kwana biyu a jihar Katsina da ke a arewa maso yammacin Najeriya.
Mutumin wanda ke da ƴaƴa 10 da matan aure biyu, ya shaida wa BBC cewa ƴan bindiga kusan 50 ne suka shiga gonarsu a ranar Lahadi da safe, inda suka kama shi tare da abokinsa da wasu mutanen da ke wasu gonakin na kusa da nasu.
"Ina cikin gonata ina girbe gero tare da abokina sai ga mutanen sun shigo a kan babura ɗauke da bindigogi, kafin mu yi wani abu har sun tattara mu sun ɗora mu a kan baburan.
''Daga nan suka kuma shiga sauran gonakin suka sace wasu mutanen suka haɗa mu duka. Kusan mu 12 suka ɗauke a ƙauyan Mallamawa," in ji shi.
''A cikinmu akwai mata huɗu, uku ƴan mata sai matar aure ɗaya, inda suka dinga bin su da ɗai-ɗai suna musu fyaɗe a gabanmu.
''Ɗaya daga cikin yaran ba ta haura shekara 10 ba kuma ko yaushe a cikin kuka take saboda fyaɗen da suka yi mata,'' in ji Adamu.
''Ita kuwa matar auren ce mata suka yi ba za su taɓa barin ta ta tafi ba saboda sun ji daɗin yin mu'amala da ita, gaskiya waɗannan mutanen ba su da imani.''

Asalin hoton, Hamisu Mallamawa
Ƴan bindigar na magana da Fulatanci
Adamu ya ce ƴan bindigar suna sanye da kayan Fulani kuma da Fulatanci suke magana, sun kuma nemi a ba su naira miliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum.
Daya daga cikin waɗanda suka tsira sun ce malmalar tuwo ɗaya ake ba su a matsayin abincin safe da rana da dare sau ɗaya.
''Abin da suke ba mu ba zan kira shi abinci ba saboda ba abin da zai maka sai dai kawai ci kar ka mutu, malmalar tuwo ɗaya ce sau ɗaya a rana.''
Musa ya ce sun samu sun gudu ne a lokacin da ƴan fashin ke barci bayan da suka kwance igiyar da aka ɗaure su da ita.
"Suna barci muka tsere ni da abokina bayan mun kwance igiyar da aka ɗaure mu, abin da ke damuna a yanzu shi ne sauran mutum 10 da muka bari a can, inda kuma a ce mun tsaya taimakonsu da yanzu yan fashin sun kama mu, shi ya sa kawai muka gudu,'' a cewar Adamu.
Adamu ya koma wajen iyalansa inda suka dinga kukan murna a lokacin da suka gan shi, ya kuma shaida wa BBC cewa zai ɗan huta kaɗan kafin ya koma gona.

Asalin hoton, Hamisu Mallamawa
Mai magana da yawun rundunar jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar wa BBC da batun tsirar mutanen, ya kuma ce suna bakin ƙoƙarinsu don ceto sauran.
Tuni mutanen jihar Katsina inda can ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya fito suka ce tura ta kai su bango, kan yawan sace-sace da kashe-kashen da ake yi musu.
A ranar 10 ga watan Yunin 2020 ne, ƴan fashi suka kashe mutum 10 a ƙaramar hukumar Faskari, sannan wata guda bayan haka aka sake kashe manoma 15 a garin Ƴargamji a dai jihar Katsinan.










